Kisan Khashoggi: Yariman Saudiyya ba shi da hankali - Sanatocin Amurka

Kisan Khashoggi: Yariman Saudiyya ba shi da hankali - Sanatocin Amurka

Sanatocin kasar Amurka sun bayyana cewa a yanzu sun hakikance cewa yariman Saudiyya na da hannu cikin kisar Jamal Khashoggi bayan da hukumar leken asirin kasar ta gabatar masu da wani bayani.

A wata caccaka da ya yi, sanata Lindsey Graham ya ce ya tabbatar Mohammed bin Salman na da hannu a cikin kisan gillar da aka yi wa dan jarida Jamal Khashoggi.

Sanatan na jam'iyyar Republican daga yankin South Carolina ya bayyana yariman na Saudiyya a matsayin mutum 'mai ta'adi', 'mahaukaci', kuma 'mai hadari'.

Kisan Khashoggi: Yariman Saudiyya ba shi da hankali - Sanatocin Amurka

Kisan Khashoggi: Yariman Saudiyya ba shi da hankali - Sanatocin Amurka
Source: Depositphotos

Saudiyya dai ta gurfanar da mutane 11 a gaban kotu, amma ta musanta cewa yariman kasar na da hannu cikin al'amarin.

Daya daga cikin sanatocin na Amurka ya ce ba zai kara goyon bayan kasar Saudiyya a yakin da take yi a Yemen ba, ko kuma sayar wa kasar da makamai, matukar yariman na kan mukaminsa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kwamishinan Ambode ya yi murabus daga APC

Wani sanatan kuma mai suna Bob Corker ya shaida wa 'yan jarida cewa a yanzu ba ya tantama ko kadan, cewa Mohammed bin Salman ne ya bayar da umurnin aiwatar da kisan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel