2019: Ma damar ba'ayi magudi ba, APC ba zata iya lashe zabe ba - tsohon hadimin Jonathan

2019: Ma damar ba'ayi magudi ba, APC ba zata iya lashe zabe ba - tsohon hadimin Jonathan

- Tsohon hadiminGoodluck Jonatahan, Dr. Doyin Okupe, ya yi ikirarin cewa babu ta yadda za'ayi jam'iyyar APC ta lashe zaben 2019, ma damar ba'ayi magudi ba.

- Okupe ya yi wannan ikirarin a ranar Talata, ya yi Allah-wadai da kin aminceewar shugaban kasa Muhammadu Buhari na sanya hannu kan dokar zabe

- Ya kuma kalubalanci jam'iyyar APC na zabar shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin dan takararta na shugaban kasa

Tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonatahan, Dr. Doyin Okupe, ya yi ikirarin cewa babu ta yadda za'ayi jam'iyya mai mulki ta APC ta lashe zaben 2019, ma damar aka yi sahihin zabe maras magudi a ciki.

Okupe ya yi wannan ikirarin a ranar Talata, ya yi Allah-wadai da kin aminceewar shugaban kasa Muhammadu Buhari na sanya hannu kan dokar zabe wacce tuni majalisun tarayya suka amince da ita.

Ya zargi shugaban kasa Buhari na kin sa hannu kan dokar, saboda kawai ya samu hanyar yin magudi a zaben 2019, yayin da su majalisun tarayya suka amince da dokar don bunkasa yadda ake gudanar da zaben, da zummar dakiloe magudi a ciki.

KARANTA WANNAN: Da dumi dumi: Jam'iyyun siyasa 45 sun goyi bayan takarar Atiku Abubakar na PDP

2019: Ma damar ba'ayi magudi ba, APC ba zata iya lashe zabe ba - tsohon hadimin Jonathan
2019: Ma damar ba'ayi magudi ba, APC ba zata iya lashe zabe ba - tsohon hadimin Jonathan
Asali: UGC

Ya kuma kalubalanci jam'iyyar APC na zabar shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin dan takararta na shugaban kasa.

"Duk wasu ayyuka na INEC ana kullasu ne kai tsaye daga Villa. Idan kuwa hakane, zuwa yanzu idan har shugaban INEC yana aiki a kashin kansa ne, to kuwa ya kyautu ace ya isarwa APC sako dama fadar shugaban kasa kan cewar basu da dan takarar shugaban kasa a zaben 2019," a cewarsa.

Okupe ya kara da cewa, "Har zuwa wannan rana, ba bisa ka'ida aka zabi shugaban kasa Buhari ba. Idan har za a zabeka a matsayin dan takarar, akwai matakan da dole sai an cika su.

"Na farko dole ne mutum ya kasance dan kasa ne. A halin yanzu kuwa, akwai wasu muhimman bayanai wanda shi kasan Buhari ya tabbatar da hakan a Poland cewar akwai masu kokonto akan asalin kasarsa, walau shi dan Nigeria ne ko dan Sudan."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel