Asirce-asirce: Hukumar yan sanda ta alanta fito-na-fito da bokaye – AIG Lawal Shehu

Asirce-asirce: Hukumar yan sanda ta alanta fito-na-fito da bokaye – AIG Lawal Shehu

Karamin mataimakin sifeton yan sanda na jihar Legas da Ogun, Lawal Shehu, a jiya ya alanta fito-na-fito da bokaye da masu siyar sassan jikin mutane a jihar kudancin Najeriya.

Wannan yaki ya zama wajibi ne bisa ga asirce-asirce, da tone-tonen kaburburan da ya yawaita kwanakin bayan nan.

Yayinda yake Magana kan yadda matasa suka shiga tsafe-tsafe, Shehu yace duk lokacin da aka kama wadannan matasa, suna ikirarin cewa wasu bokaye ne suka sanyasu. Wannan na nuna cewa bokaye ne babban ummul haba’isin wannan aika-aika.

KU KARANTA: Dan sarkin Kano, Aminu Sanusi zai angonce; kalli zafafan hotunansa

Yace: “Idan malaman gargajiya ne, me sukeyi da sassan jikin mutane? Mun kama wasu ranan 3 ga watan Disamba misalin karfe 8:30 na dare da kan mutum.”

“Mun samu labari cewa wani mai suna Jimoh Adeola dake gadin makabartan Musulmai dake Oke Yadi, Abeokuta jihar Ogun na da sassan jikin mutane kuma ya dade yana wannan kasuwanci.”

“An damke mutane biyar kuma an gano abubuwa da yawa a hannunsu. Wadanda aka kama sune Lukmon Bayewunmi, Kabir Badmus, Victor Nnacheta and Nurudeen Sogaolu.”

“An gano haban mutum da kan mutum a hannunsu. Za’a gurfanar da sub a da dadewa ba.”

Hukumar yan sandan Najeriya ta cika hannu da wannan mai gadin makabartan da ake zargin yana hakan kaburbura yana sace sassan jikin mutane.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel