Kada wanda ya sake ya taba makiyayan kasar Malin da suka bayyana a Sokoto – Miyetti Allah sunyi gargadi

Kada wanda ya sake ya taba makiyayan kasar Malin da suka bayyana a Sokoto – Miyetti Allah sunyi gargadi

Kungiyar kare hakkin Fulani Makiyaya, Miyetti Allah Kautal Horey, ta gargadi jami’an tsaron Najeriya da masu farin hula kan taba makiyayan kasar Malin da suka bulla a karamar hukumar Gudu da Tangaza da ke jihar Sokoto.

A makon da ya gabata, rahotannin sun yawaita a kafafen yada labarai cewa wasu yan bindiga sun bulla a jihar Sokoto rana Juma’a.

Amma hukumar yan sandan jihar ta yi watsi da wadannan rahotanni cewa ba yan bindiga bane, innama wasu makiyaya ne da ke zaune a dajin Nijar dake da iyaka da karamar hukumar Gudu da kuma Tangaza na jihar Sokoto.

KU KARANTA: Ma'aikatan majalisar dokoki sun hana majalisa zama, suna zanga-zanga

Sakataren kungiyar Miyetti Allah Kautal Horey, Alhassan Saleh, ya bayyanawa manema labarai cewa kada kowa da ya damu da makiyayan kasar Malin da suka nayyana a Najeriya. Kawai suna kiwo ne da suka saba shekaru 100 baya yanzu.

Yace: “Wadannan bay an bindiga bane; kundin tsarin kungiyar ECOWAS ya bada daman yan kasashe mambobin kungiyar su shiga inda suke so domin kiwo. Sun kasance suna kiwo shekaru dari baya. Su kan zo lokacin rani kuma su koma daga baya.”

Saleh ya ce ya kamata gwamnatin tarayya da jami’an tsaro su wayar da kan mutane kan wannan yarjejeniya ta ECOWAS domin kawar da wani rikici da ka iya faruwa.

Yace: “Ina addu’an kada wanda ya taba su ya jawo mana tashin hankali.”

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel