Tsarin Allah: Tsohon minista da kakakin majalisa sun sha da kyar a wani harin bangar siyasa

Tsarin Allah: Tsohon minista da kakakin majalisa sun sha da kyar a wani harin bangar siyasa

- Yan barandan siyasa sun kutsa gidan tsohon ministan harkokin masana'antu, Bello Maitama, inda suka lalata masa motoci guda biyu da ta kakakin majalisar jihar Jigawa

- Yan bangar siyasar sun kai wannan hari ne a lokacin da tsohon ministan yake jagorantar zaman sulhu na mambobin jam'iyyar APC a jihar

- Sai dai, mai magana da yawun rundunar 'yan sanda a jihar Jigawa, Audu Jinjiri, ya bayyana rundunar yan sanda ta cafke mutane 10 da ke da hannu a kai harin

Yan barandan siyasa sun kutsa gidan tsohon ministan Nigeria kan harkokin masana'antu, Bello Maitama, inda suka lalata masa motoci guda biyu da kuma ta kakakin majalisar dokoki ta jihar Jigawa, Isa Idris.

Mr. Maitama, ministan masana'antu a mulkin soji, karkashin Ibrahim Babangida, na jagorantar wani taron sulhu da mambobin APC da suke ganin ba'ayi masu dai-dai ba a bangarori da dama na tafiyar jam'iyyar a gidansa da ke karamar hukumar Gwaram, ba tare da sani hawa ko sauka ba, 'yan bangar siyasar suka kutsa dakin taron tare da farwa tsohon ministan.

Wani da lamarin ya faru a gabansa, wanda yake cikin kwamitin sulhun, ya shaidawa manema labarai cewa sai da aka kai ruwa rana, tare da taimakon jami'an tsaro kana aka samu damar fitar da tsohon ministan da kakakin majalisar daga cikin gidan, sai dai an lalata motocinsu.

KARANTA WANNAN: 2019: PDP da sauran jam'iyyu zasu tarwatse, suna ji suna gani Buhari zai zarce - The Economist

Tsohon minista da kakakin majalisa sun tsallake rijiya ta baya baya: Mutane 5 sun jikkata
Tsohon minista da kakakin majalisa sun tsallake rijiya ta baya baya: Mutane 5 sun jikkata
Asali: Twitter

Ya ce sai da jami'an tsaron suka rinka yin harbi a saman iska kana suka samu damar tarwatsa tawagar 'yan bangar siyasar, yana mai ruwaito cewa idan da ace basu yi hakan ba, to kuwa lamarin ya munana.

A baya baya, Gwamna Mohammad Badaru na jihar, ya kafa kwamitin sulhu wanda zai hada kawunan 'yayan jam'iyyar musamman wadanda ke fushi da jam'iyyr a jihar, wanda kuma tsohon ministan yake a matsayin shugaban kwamitin.

Wani da lamarin ya afku a gabansa, ya shaidawa manema labarai cewa, an dade ana samun tashin hankula a Gwaram tun bayan da gwamnatin jihar ta dora wani sabon shugaban karamar hukumar. Ya yi zargin cewa sabon shugaban karamar hukumar baya tafiya da mambobin jam'iyyar, musamman wadanda suka yiwa jam'iyyar hidima tun daga tushe.

KARANTA WANNAN: Boko Haram: Har yanzu muna fuskantar hare hare - Shehun Borno ya shaidawa Buhari

Cikin tsarewar Allah, shugaban karamar hukumar da mataimakinsa, sun tsallake ta katangar bayan gidan, sai dai 'yan bangar siyasar sun lalata motocinsu.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sanda a jihar Jigawa, Audu Jinjiri, ya bayyana lamarin a matsayin rikici tsakanin bangarorin 'yan bangar siyasa guda biyu, jim kadan bayan taron sulhun da tsohon ministan ya jagoranta.

Ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a karshen makon da ya gabata, kuma rundunar ta samu nasrar cafke mutane 10 da ake zargi da sa hannu a rikicin.

Ya ce mutane 5 sun jikkada a harin, wadanda ke samun kulawa a asibiti.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel