Yanzu Yanzu: Mutane da dama sun mutu yayinda rikici ya barke a garuruwan Cross River

Yanzu Yanzu: Mutane da dama sun mutu yayinda rikici ya barke a garuruwan Cross River

Wani rikici da ya barke a garuruwa hudu da ke karamar hukumar Biase, jihar Cross River ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama sannan da dama sun ji rauni, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Daruruwan mata da yara sun zamo marasa galihu sanadiyar rikicin wanda ya barke a ranar Litinin a , Egbor, Ipene, da kuma Abanwan, garuruwa hudu cilin 10 da ke Erei.

Wani mazaunin yankin ya bi ba’asi rikicin zuwa siyar da wani fili, wanda ake amfani wajen shukan bishiyoyin kwakwa tun 1973.

An tattaro cewa filin mallakar garuruwan Urugbam da Egbor ne, amma sai garin Egbor suka bayar da shi ga ma’aikatar African Stone Works Ltd., ba tare da sanin Urugbam da sauran garuruwan da ke amfana daga wajen tun sama da shekaru 45 ba.

Yanzu Yanzu: Mutane da dama sun mutu yayinda rikici ya barke a garuruwan Cross River
Yanzu Yanzu: Mutane da dama sun mutu yayinda rikici ya barke a garuruwan Cross River
Asali: Depositphotos

Mazauna yankin sun zargi jami’an tsaro da rashin shiga lamarin rikicin da wuri, wanda suka ce yana ci gaba da faruwa har karfe 9:00 na safiyar ranar Talata.

KU KARANTA KUMA: Babu wanda Atiku ya fada ma cewa ya karbi bizan Amurka – Jami’in kungiyar kamfen

Kwamishinan yan sandan Cross River, Hafiz Inuwa ya bayyana cewa mumunan rikici ya barke amma an tura jami’ai domin su kwantar da tarzoman.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel