An hana kowa yin dawafi sai masu nakasa a Ka'aba
Rahotanni sun kawo cewa masu kula da Masallatai biyu mafi daraja na kasar Saudiyya sun ware tsawon sa'a biyu inda suka bai wa masu nakasa damar yin dawafi su kadai a ranar Litinin, 3 ga watan Disamba.
Ma'aikatar ta yi hakan ne domin nuna nakasassun a ranar masu nakasa ta duniya wacce ake gudanarwa a ranar 3 ga watan Disamba ta kowace shekara.
Jaridar Saudi Gazette ta ruwaito sakataren ma'aikatar Mashour Al-Monaami, na cewa hakan na nuna yadda Masarautar kasar ke mutunta wadannan mutane a cikin jama’a da kuma ba su hakkokinsu.
Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar ce domin mayar da hankali kan irin hali da kalubalen da masu nakasa ke ciki a kowane fanni na rayuwa a duniya.
KU KARANTA KUMA: Ya kamata Buhari ya fallasa wadanda su ka nemi kujerar sa tun kafin ya bar Duniya – Shehu Sani
Taken ranar ta bana shi ne: "Tallafawa mutane masu nakasa da kuma da kuma tabbatar da daidato."
Yawanci dai wajen dawafi na yawan cika da mutane ta yadda ko yaushe sai dai masu lalura ko masu nakasa su hau can sama su yi nasu dawafin.
Saudiyya ta kafa wasu dokoki tare da bayar da kulawa ga mutane masu nakasa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng