Shugaba Buhari ya gabatar da jawabi a kasar Poland (Hotuna)

Shugaba Buhari ya gabatar da jawabi a kasar Poland (Hotuna)

Mun kawo muku rahoton cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya tafi birnin Katowice, kasar Poland, ranan Asabar domin halartan taron gangamin duniya kan canjin yanayi karo na 24 na majalisar dinkin duniya wato UNFCCC.

Wannan taro na shugabannin duniya zai gudana ne daga rana 2 ga watan Disamba zuwa 5.

Hadimin shugaba Buhari kan sabbin kafafen yada labarai, Bashir Ahmad, ya sanar da cewa shugaban kasan Najeriya ya gabatar da dogon jawabi ga shugabannin duniya a ranan Litinin, 3 ga watan Disamba, 2018.

Shugaba Buhari ya gabatar da jawabi a kasar Poland (Hotuna da Bidiyo)
Shugaba Buhari ya gabatar da jawabi a kasar Poland (Hotuna da Bidiyo)
Asali: Facebook

Buhari ya bayyana matakan da gwamnatin Najeriya ke dauka wajen dakile hadarin canjin yanayi a nahiyar Afrika da duniya gaba daya.

Shugaba Buhari ya gabatar da jawabi a kasar Poland (Hotuna)
Shugaba Buhari ya gabatar da jawabi a kasar Poland (Hotuna)
Asali: Twitter

Shugaba Muhammadu Buhari ya mayar da martani mai zafi kan masu rade-radin cewa ya mutu a shekarun baya da yayi jinya a kasar Ingila. Ya bayyana cewa yana nan da rai kuma ba da dadewa ba, zan yi murnan ranan haihuwa na cika shekaru 76.

Yace: "Daya daga cikin tambayoyin da aka min yau a ganawata da yan Najeriya mazauna Poland shine shin ni ne ko wani na ne kirkirarre. Wannan jahilcin ba abun mamaki bane - lokacin da nike jinya a bara, mutane da yawa sun so in mutu."

" Ni ne nan.... Ba da dadewa ba a cikin watan ne, zanyi murnan cika shekaru 76 kuma ina nan daram dam-dam."

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel