Gangamin PDP: Atiku, Saraki, Dogara da sauran jiga jigai sun dira jahar Sakkwato (Hotuna)

Gangamin PDP: Atiku, Saraki, Dogara da sauran jiga jigai sun dira jahar Sakkwato (Hotuna)

A yau ne ake yinta a garin Sakkwato ta jahar Sakkwato, inda tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar yake kaddamar da takararsa ta shugaban kasa tare da yakin neman zabensa na yankin Arewa maso yammaci.

An hangi dubunnan masoya da magoya bayan Atiku Abubakar cikin wata doguwar ayarin motoci dauke da fentin jam’iyyar PDP, suna wake wake ga kuma sautin wakokin takarar Atiku Abubakar daban daban suna fita daga lasifika daban daban.

KU KARANTA: Da ɗumi ɗumi: An naɗa sabon Kaakakin majalisar dokokin jahar Katsina

Gangamin PDP: Atiku, Saraki, Dogara da sauran jiga jigai sun dira jahar Sakkwato (Hotuna)

Atiku
Source: Facebook

Legit.com ta ruwaito da misalin karfe goma sha biyu na rana ne aka tsammaci isar Atiku Abubakar garin Sakkwato, sai dai an samu akasi ta yadda sai karfe 2 na rana ya isa garin, inda isarsa keda wuya ya garzaya filin taro, dandalin Shehu Kangiwa.

Yawancin mahalarta taron masoya da magoya baya ne da kuma yayan jam’iyyar PDP da suka fito daga jihohin yankin Arewa maso yammacin Najeriya, da suka hada da Sokoto, Zamfara, Kebbi, Jigawa, Katsina, Kano da jahar Kaduna.

Gangamin PDP: Atiku, Saraki, Dogara da sauran jiga jigai sun dira jahar Sakkwato (Hotuna)

Atiku
Source: Facebook

Daga cikin manyan baki da suka halarci wannan taro akwai tsohon mataimakin gwamnan jahar Sakkwato Alhaji Muntari Shagari, shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki, Kaakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara, gwamnan Sakkwato Aminu Waziri da Ahmad Makarfi.

Haka zalika akwai gwamnonin PDP da suka hada Darius Ishaku na Taraba, Ibrahim Dankwambo na Gombe, Samuel Ortom na Benuwe sai kuma tsofaffin gwamnonin PDP da suka hada da Sule Lamido, Ibrahim Shehu Shema, shugaban jam’iyyar PDP, Uche Secondus da sauran iyayen jam’iyyar.

Gangamin PDP: Atiku, Saraki, Dogara da sauran jiga jigai sun dira jahar Sakkwato (Hotuna)

Atiku
Source: Facebook

Sauran sun hada da shuwagabannin jam’iyyar PDP na jihohin Sokoto, Zamfara, Kebbi, Jigawa, Katsina, Kano da jahar Kaduna, yan majalisun jam’iyyar PDP na jihohin Sokoto, Zamfara, Kebbi, Jigawa, Katsina, Kano da jahar Kaduna, da kuma sauran shuwagabannin PDP na yankin.

Daga karshe ana sa ran Atiku Abubakar zai kaddamar da babban ofishin takararsa na jahar Sakkwato bayan kammala taron.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel