Wanzami ya farke cikin wani mutum da ya je zance wurin wata budurwar a Katsina

Wanzami ya farke cikin wani mutum da ya je zance wurin wata budurwar a Katsina

Abdulrahman Sani, mai shekaru 40, ya gamu da ajalinsa bayan wani mutum ya farke masa ciki da wuka a garin Daura, jihar Katsina.

Sani ya gamu da ajalinsa ne ranar Juma'a, a hanyar sa ta komawa gida, bayan ziyartar budurwar sa.

Duk da jami'an rundunar 'yan sanda sun kama mutumin da ya kashe Sani, sun bayyana cewar ba su da masaniyar dalilin da yasa ya kashe marigayin.

Marigayin, mazaunin unguwar Kwari da ke garin Daura, ya gamu da ajalinsa ne bayan ya yi sallama da masoyiyar sa, Amina Suleiman, da ya ziyarta a unguwar Kurunbai.

Wanzami ya farke cikin wani mutum da ya je zance wurin wata budurwar a Katsina

Wanzami ya farke cikin wani mutum da ya je zance wurin wata budurwar a Katsina
Source: Depositphotos

Rahoton jami'an 'yan sanda ya bayyana cewar mutumin da ya kashe Sani, ya labe ne a cikin duhu tare da jiransa ya kammala zance da Amina kafin ya caka masa wuka a ciki.

DUBA WANNAN: An gargadi limaman Coci da ba za su daina luwadi ba su ajiye aiki

Amina ta shaidawa jami'an 'yan sanda cewar wani matashi ne mai suna Sani Salisu (mai shekaru 28) ya kashe masoyin nata bayan sun yi sallama. Amina ta ce a kan idonta lamarin ya faru.

Yanzu haka an mayar da mai laifin zuwa hedkwatar hukumar 'yan sanda da ke Katsina domin cigaba da bincike.

Ana tuhumar mai laifin da aikata kisan kai, laifin da hukumar 'yan sanda ta ce ya saba da sashe na 221 na kundin fenal kod.

Dan sanda mai gabatar da kara, Insifekta Sani Ado, ya shaidawa kotun majistare da ke Katsina cewar har yanzu su na gudanar da bincike a kan mai laifin tare bukatar kotun ta basu karin lokaci zuwa ranar 22 ga watan Janairu na shekarar 2019.

Alkaliyar kotun, Hajiya Fadile Dikko, ta amince da bukatar hukumar 'yan sandan tare da bayar da umarnin tsare mai laifin a gidan yari har zuwa ranar 22 ga watan Janairu da kotun za ta cigaba da sauraron shari'ar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel