2019: Willie Obiano ya karyata masu cewa yana goyon bayan Buhari da Atiku

2019: Willie Obiano ya karyata masu cewa yana goyon bayan Buhari da Atiku

- Gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano, ya koka kan rahotannin da ake yadawa na cewar yana goyon bayan Muhammadu Buhari da kuma Alhaji Atiku Abubakar

- Ya jaddada cewa shi yana goyon bayan dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar APGa, Janar John Gbor, a zabe mai zuwa

- Sanarwar ta ce babu yadda za ace Obiano, a matsayinsa na shugaban kwamitin amintattu na APGA, ace kuma yana goyon bayan wasu 'yan takara bana jam'iyyarsa ba

Gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano, wanda ya koka kan rahotannin da ake yadawa na cewar yana goyon bayan takarar jam'iyyar APC, shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019, da kuma Alhaji Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP.

Obiano ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa daga kwamishinan watsa labarai da hulda da jama'a, C-Don Adinuba, da aka rabawa manema labarai a Akwa, jihar Anambra.

Ya jaddada cewa shi yana goyon bayan dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar APGa, Janar John Gbor, a zabe mai zuwa.

KARANTA WANNAN: 2019: Wata kungiya tayiwa Atiku alkawarin kashi 90 na kuri'un jihar Cross River

2019: Willie Obiano ya karyata masu cewa yana goyon bayan Buhari

2019: Willie Obiano ya karyata masu cewa yana goyon bayan Buhari
Source: Depositphotos

Ya kuma bayyana labaran da ake yadawa na cewar yana goyon bayan PDP ko APC a zabe mai zuwa, a matsayin "labaran kanzon kurege".

Sanarwar ta ce abun zai zama almara idan aka ce Obiano, a matsayinsa na shugaban kwamitin amintattu na jam'iyyar APGA a ce wai zai goyin bayan wasu 'yan takara bana jam'iyyarsa ba, don haka sanarwar tace ala tilas ne ga gwamnan ya goyin bayan dan takarar shjugaban kasa karkashin jam'iyyar APGA.

Sanarwar ta yi nuni da cewa ba kamar a zabukan da suka gabata ba, a lokacin da APGA bata da dan takarar shugaban kasa kuma hakan ya tilasta mata marawa jam'iyya mai mulki baya a lokacin, amma a zaben 2019, a cewar sanarwar, APGA na da dan takararta da 'yan Nigeria za su zaba.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel