2019: Wata kungiya tayiwa Atiku alkawarin kashi 90 na kuri'un jihar Cross River

2019: Wata kungiya tayiwa Atiku alkawarin kashi 90 na kuri'un jihar Cross River

- Kungiyar Atiku Shall Lead Nigeria, ta dau alkawarin tarawa dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar, kashi 90 na kuri'un jihar Cross River

- Kungiyar wacce take da rassa a fadin jihohin kasar, ta kunshi mutane masu ra'ayi daya da kuma son ganin an ceto kasar daga matsalolin rugujewar tattalin arziki da take ciki

- A cewar kungiyar, Nigeria na fuskantar matsaloli masu girman gaske kuma tana da yakinin cewa sai 'yan siyasa irin Atiku ne zasu iya magance wadannan matsaloli

A ci gaba da fuskantar zabukan 2019, daraktan kungiyar "Atiku Shall Lead Nigeria" (Atiku zai shugabanci Nigeria), Mr Patrick Agida, ya dau alkawarin tarawa dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, kashi 90 na kuri'un jihar Cross River.

Da ya ke jawabi a lokacin kaddamar da wani shiri na yakin zaben gida-gida na kungiyar a Calabar, a ranar Lahadi, Agida ya bayyana cewa nasarar Atiku ta lashe zaben 2019 na da karfin gaske a jihar duba da irin ayyukan raya kasa da Gwamna Ben Ayade ya shimfida a jihar.

Ya ce kungiyar wacce take da rassa a fadin jihohin kasar, ta kunshi mutane masu ra'ayi daya da kuma son ganin an ceto kasar daga matsalolin rugujewar tattalin arziki da take ciki.

KARANTA WANNAN: Boko Haram: Har yanzu muna fuskantar hare hare - Shehun Borno ya shaidawa Buhari

2019: Wata kungiya tayiwa Atiku alkawarin kashi 90 na kuri'un jihar Cross River
2019: Wata kungiya tayiwa Atiku alkawarin kashi 90 na kuri'un jihar Cross River
Asali: Depositphotos

A cewarsa, kungiyar ta hada kan mambobinta da ke fadin kasar zuwa akwatunan zabe don tabbatar da cewa an kasa an tsare kuri'un da aka kadawa Atiku.

"Nigeria na fuskantar matsaloli masu girman gaske kuma muna da yakinin cewa sai 'yan siyasa irin Atiku ne zasu iya magance wadannan matsaloli.

"A matsayinmu na kungiyar siyasa, mun yi alkawarin tarawa Atiku kashi 90 na kuri'un Cross River. Kungiyar dai na da rassa a fadin kasar, muna da matakin shugabanci a kasa, shiyya, da kuma jiha, gunduma da akwatunan zabe." a cewarsa.

Ya ce Atiku zai farfado da tattalin arziki tare da samar da tsaro ga al'umar Nigeria idan har aka zabe shi a matsayin shugaban kasa, inda ya kara da cewa idan har aka samu ingantaccen tattalin arziki da tsaro, to sauran fannoni a kasar zasu bunkasa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel