Yanzu Yanzu: Babban dan kasuwa a Kebbi Asaija ya jagoranci yan APC 5,000 zuwa PDP

Yanzu Yanzu: Babban dan kasuwa a Kebbi Asaija ya jagoranci yan APC 5,000 zuwa PDP

Wani shahararren dan kasuwa a Kebbi, Alhaji Mustapha Asaija, da wasu mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) dubu biyar sun bar jam’iyyar zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Sanata Isa Galaudu, dan takarar kujeran gwamna a PDP, da mataimakinsa, Alhaji Abubakar Malan, jami’ansu da yan jam’iyyar adawa da dama a jihar ne suka tarbi dan kasuwar da magoya bayansa a Ambursa da ke karaar hukumar Birnin Kebbi, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Asaija ya bayyana cewa ya bar jam’iyyar APC mai mulki tare da magoya bayansa zuwa PDP saboda jam’iyyar ta gaza inganta rayuwar yan Najeriya duk da tarion alkawaran da ta dauka.

Yanzu Yanzu: Babban dan kasuwa a Kebbi Asaija ya jagoranci yan APC 5,000 zuwa PDP

Yanzu Yanzu: Babban dan kasuwa a Kebbi Asaija ya jagoranci yan APC 5,000 zuwa PDP
Source: Depositphotos

Ya bayyana cewa zai kara kawo tarin mutane a yankin domin ganin nasarar Isa Galaudu a zaben 2019.

KU KARANTA KUMA: Ta bayyana: Gaskiyar dalilin da ya sa Atiku bai tafi Amurka ba

Da yake tarban masu sauya shekar, Galaudu ya nuna farin ciki sannan ya yi kira ga kamfen cikin zaman lafiya tare da gargadi akan kalamun kiyayya da rikici.

Ya kuma yi alkawarin cewa idan har a zabe shi zai inganta rayuwar matasa da al’umman jihar ta hanyar yi masu duk wasu ayyuka da za su kawo ci gaba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel