Bayan kwanaki 107: Matasa a Kebbi sun gano adadin kwayar gero dake cikin buhu daya

Bayan kwanaki 107: Matasa a Kebbi sun gano adadin kwayar gero dake cikin buhu daya

- A ranar Asabar, bayan shafe kwanaki 107, matasa daga karamar hukumar Yawuri ta jahar Kebbi sun kammala kidayar adadin kwayar gero dake cikin buhu daya

- Matasan sun gano cewa akwai kwayar gero 11,979,868 a cikin buhu daya, yayin da suka gano cewa akwai kwaya 2,395,973,6 a cikin dami daya na geron

- Majiyar Legit.ng ta ruwaito muku cewa muhawarar ta kaure a tsakanin matasan akan 'wai tsakanin buhun gero da al’ummar jama’an dake kasar Najeriya wanene yafi yawa'

Kwanaki 107 da suka wuce, wasu matasa daga karamar hukumar Yawuri ta jahar Kebbi dake Arewa maso yammacin Najeriya suka dukufa wajen kirga adadin kwayar gero dake cikin buhun gero guda daya don kashe wata zazzafar muhawara data kaure a tsakaninsu.

Littafin da matasan suka tsara na musamman kan kidayarsu
Littafin da matasan suka tsara na musamman kan kidayarsu
Asali: Twitter

A ranar Asabar, bayan shafe kwanaki 107 matasan na kidayar buhun geron, sun kammala, tare da yin bukin sanar da sakamakon kirgar da suka yi, inda suka gano cewa akwai kwayar gero 11,979,868 a cikin buhu daya na geron da suka kirga.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito muku cewa muhawarar ta kaure a tsakanin matasan akan 'wai tsakanin buhun gero da al’ummar jama’an dake kasar Najeriya wanene yafi yawa', anan ne fa aka ja layi, wasu na ganin jama’an Najeriya sun fi yawa, wasu kuma suka ce a’a buhun gero yafi yawa.

KARANTA WANNAN: Hanyoyin da zamu taimakawa Ganduje har Buhari ya samu kuri'u 5m a Kano - Gude

Matasan da suka shafe watanni 6 suna kirga buhun gero
Matasan da suka shafe watanni 6 suna kirga buhun gero
Asali: Twitter

Cikin wata sanarwa daga gwamnatin jihar Sokoto da ta saki a shafinta na Twitter, ta bayyana cewa sanin cewa akwai kwayar gero 11,979,868 a cikin buhu daya na geron, ya dauki matasan watanni shida, wanda kuma hakan ne ya kawo karshen muhawararsu, tare da cimma matsaya kan cewar adadin 'yan Nigeria ya zarce adadin geron da ke cikin buhu daya.

Daga cikin wadanda suka halarci taron bukin bayyana sakamakon wanna kidaya, akwai Farfesa Aliyu Muhammad Bunza, wanda ya kasance bako na musamman mai jawabi, sai kuma mai martaba Sarkin Yauri, Dr. Zayyanu Abdullahi, wanda ya jinjinawa matasan akan wannan namijin kokari nasu.

Bayan kwanaki 107: Matasa a Sokoto sun gano adadin kwayar gero dake cikin buhu daya
Bayan kwanaki 107: Matasa a Sokoto sun gano adadin kwayar gero dake cikin buhu daya
Asali: Twitter

Haka zalika, wannan gagarumin buki ya samu halartar gwamnan jihar Kebbi, Sanata Atiku Bagudu wanda ya samu wakilcin kwamishinan watsa labarai na jihar, Hon. Gado Marafa.

Matasan dai su 37 ne suka gudanar da wannan aikin kidayar, inda suka kuma gano cewa akwai kwayar gero 2,395,973,6 a cikin dami daya na gero.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng