Ku daina matsawa Buhari kan sanya hannu a dokar zabe – Shugaban masu rinjaye a majalisa

Ku daina matsawa Buhari kan sanya hannu a dokar zabe – Shugaban masu rinjaye a majalisa

Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Alhaji Ahmed Lawan ya shawarci jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta dakatar da matsawa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan sanya hannu akan dokar zaben 2019.

Lawan ya bayar da shawarar ne a lokacin da yake amsa tambaya sa ga manema labarai na majalisa a Abuja a ranar Juma’a, 30 ga watan Nuwamba.

Ku daina matsawa Buhari kan sanya hau a dokar zabe – Shugaban masu rinjaye a majalisa
Ku daina matsawa Buhari kan sanya hau a dokar zabe – Shugaban masu rinjaye a majalisa
Asali: Facebook

Ya yi gargadin cewa shugaban kasar ba zai sanya hannu a dokan zabe batare da nazarin takardun ba don guje ma kura-kurai.

KU KARANTA KUMA: Da ni da Bishop Crowther daya mu ke, daga tsatson annabi Ibrahim mu ka fito - Buhari

A cewarsa, dokar zaben 2006 da aka gyara da shine aka yi amfani wajen gudanar da zaben 2015 kuma har yanzu ana iya amfani da shi wajen gudanar da zaben 2019.

A wani lamari na daban, mun ji cewa dan majalisa mai wakiltan Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawan kasar, Shehu Sani ya yi watsi da kiran da gwamnatin tarayya ta yi wa kasar ASmurka kan batun ba dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party, Atiku Abubakar biza.

Legit.ng ta tattaro cewa gwamnatin tarayya ta fada ma kasar Amurka cewa ta hankalta wajen ba Atiku biza don kada hakan ya sa a ga kamar ta marawa tsohon mataimakin shugaban kasar baya a zaben 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel