Da ni da Bishop Crowther daya mu ke, daga tsatson annabi Ibrahim mu ka fito - Buhari

Da ni da Bishop Crowther daya mu ke, daga tsatson annabi Ibrahim mu ka fito - Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya caccaki wadanda ke zarginsa da yunkurin musuluntar da Najeriya inda ya bayyana kan shi a matsayin tsatson annabi Ibrahim kamar Bishop Crowther.

Crowther shine limamin Anglican na farko a Najeriya. Shine ya fassara injila daga Turanci zuwa yaren Yarbaci.

A wani rubutu da jaridar Kirista na Amurka ta wallafa, Buhari ya bayyana zargin a matsayin “shirme”.

Da ni da Bishop Crowther daya mu ke, daga tsatson annabi Ibrahim mu ka fito - Buhari
Da ni da Bishop Crowther daya mu ke, daga tsatson annabi Ibrahim mu ka fito - Buhari
Asali: Depositphotos

Shugaban kasar ya bayyana cewa abunda ya hada Musulmi da Kirista a duniya ya fi wanda ya raba su nesa ba kusa ba.

KU KARANTA KUMA: NAFDAC ta kama kwayoyin tramadon da kudin sa ya kai N193bn a shekara 1

Ya ce ya zama dole yan Najeriya su guji duk wani son zuciya a tsakaninsu “domin sai mu hada kanmu ne za mu cimma nasara.”

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel