Yahoo Yahoo: An gurfanar da 'yan Nigeria 2 a Ghana da laifin damfara ta yanar gizo

Yahoo Yahoo: An gurfanar da 'yan Nigeria 2 a Ghana da laifin damfara ta yanar gizo

- Wata kotu da ke da zama a birnin Accra, Ghana ta bada belin wasu 'yan Nigeria guda biyu da wata 'yar Ghana daya, akan kudi N68,184,506 tare da wakilai guda 4

- Ana tuhumarsu ne akan aikata laifukan da suka jibinci damfara. Sai dai, sun karyata wannan zargi da ake masu

- Mai shigar da kara ya ce tsakanin shekarar 2016 da 2017, Enameguno, Fauziya, da Odjegba, sun damfari Maria J. Pizaaro GH¢536,191.87 da Brunilda J. Rodriguez GH¢392.781.37

Wata kotu da ke da zama a birnin Accra, Ghana ta bada belin wasu 'yan Nigeria guda biyu, Victor Manu Enameguno, Kingsley Odjegba da kuma wata 'yar kasar Ghana, Fauziya Yussif, akan kudin kasar Ghana GH¢930,000 wanda yayi dai dai da N68,184,506 tare da wakilai guda 4.

Ana tuhumarsu ne akan aikata laifukan da suka jibinci damfara. Sai dai, sun karyata wannan zargi da ake masu, na hadin kai tare da yin damfara, damfara ta hanyar bayanan karya, safarar makudan kudade ba bisa ka'ida ba, da kuma aikata ta'addanci.

Charles Wilcox Ofori, babban lauyan hukumar da ke yaki da masu tu'annadi da dukiyar jama'a, ya sanar da kotun cewa wadanda ake zargin Enameguno, Odjegba 'yan Nigeria ne, wadanda basu da wani aiki ko kasuwanci a Ghana, yayin da ita Yussif yar kasar ce.

KARANTA WANNAN: Da dumi dumi: Jam'iyyar APGA ta dare gida biyu, sabon rikici ya mamaye jam'iyyar

Yahoo Yahoo: An gurfanar da 'yan Nigeria 2 a Ghana da laifin damfara ta yanar gizo
Yahoo Yahoo: An gurfanar da 'yan Nigeria 2 a Ghana da laifin damfara ta yanar gizo
Asali: Depositphotos

Ya ce a tsakanin shekarar 2016 da 2017, Enameguno, Fauziya, da Odjegba, sun damfari Maria J. Pizaaro GH¢536,191.87 da Brunilda J. Rodriguez GH¢392.781.37 ta hanyar yanar gizo da sunan zasu kulla alakar kasuwanci da su.

Lauyan hukumar ya ce a ranar 27 ga watan Mayun wannan shekarar, hukumar EOCO ta samu rahoto a ranar 1 ga watan Maris daga cibiyar kwararrun jami'ai, wanda ya nuna cewa Enameguno da Fauziya kwastomomi ne a Ecobank Ghana Limited kuma sun samu saon kudi har GH¢928,973.24 daga shaidar lauyan a kasar Amurka, bayan da suka yaudareshi da bayanan karya.

Mai shigar da karar ya bayyana cewa bincike ya tabbatar da cewa Odjegba ne ya karbi kason kudin na karshe.

Ya ce Fauziya ta karbi GH¢536,192.87 daga Maria J. Pizarro, wacce ta tura mata a asusunta na banki.

Haka zalika Fauziya, tare da Enameguno sun damfari Brunilda J. Rodriguez har GH¢392,781.37 tsakanin watan Mayu da Oktoba na shekarar 2017.

Ya ce a yayin binciken sun gano cewa Enameguno da Fauziya suna soyayya, don haka kotun, karkashin mai shari'a Madam Ruby Naa Aryeetey, ta bukaci Fauziya ta yi gwajin ciki, kana ta bukaci gaba daya wadanda ake zargin guda biyu da su hadu da mai bincike kafin ranar sauraron shari'ar na gaba.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel