Majalisar Tarayya ta fiye tsanani da rashin godiya - NNPC

Majalisar Tarayya ta fiye tsanani da rashin godiya - NNPC

Kamfanin Man fetur na kasa watau NNPC, ya yi zargi tare da kalubalantar Majalisar Tarayyar Najeriya kan tsanani gami da rashin godiya dangane da dambarwar karanci da wahalhalu na rashin wadatuwar man fetur da ta auku cikin kasar nan a shekarar da ta gabata.

Kamar yadda shafin jaridar This Day ya ruwaito, kamfanin na NNPC na zargin majalisar tarayyar kasar nan dangane da rashin godiya da kuma tsanantawa yayin da ta bayar da umarnin kawo karshen wahalhalu da karancin man fetur a shekarar 2017 da ta gabata.

Majalisar ta nuna hali na rashin yabawa kamfanin yayin da ya yi gaggawa ta tabbatar da kiyayewa tare da yi umarnin ta da'a wajen kawo karshen kalubalai na karancin man fetur a kasar nan.

Shugaban Kamfanin NNPC; Maikanti Baru
Shugaban Kamfanin NNPC; Maikanti Baru
Asali: UGC

A madadin yabo, majalisar cikin tsanantawa ta kalubalanci kamfanin na NNPC da rashin aikata daidai yayin tabbatar da umarnin ta na kawo karshen tagayyara da cuzgunin al'umma dangane da rashin wadatar man fetur a manyan biranen kasar nan.

Yayin ganawarsa da manema labarai, shugaban kamfanin man fetur na kasa Maikanti Baru, shine ya bayyana hakan cikin babban birnin tarayya na Abuja.

KARANTA KUMA: Ba bu wata kitimurmura ta tsige Gwamna Emmanuel - APC

Dakta Baru ya bayyana cewa, ba a iyawa majalisar tarayyar da al'ummar kasar nan da a halin yanzu su ke da mummunar fahimta ta rashin yabawa jajircewa da kuma kwazon kamfanin na NNPC duk da mashahurancinsa ta kulawa da dukiyar gwamnati a bayyane.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, hukumar kiddiga kan Alkaluma ta kasa watau NBS, National Bureau of Statistics, ta bayyana yadda gwamnatin Najeriya ta batar da N900bn wajen shigo da Lita Biliyan 4.37 ta man fetur a ma'adanansa cikin kasar nan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel