Daga karshe: EFCC ta mikawa 'First Bank' motoci 116 da gidaje 20

Daga karshe: EFCC ta mikawa 'First Bank' motoci 116 da gidaje 20

- EFCC ta mika motoci 116 da gidaje 20 a jihohin Edo, Rivers da Legas da ta kwato daga hannun wani mutumi mai suna Michael Obasuyi ga 'First Bank Plc.'

- Haka zalika, an gurfanar da Osasogie tare da wasu kamfanoninsa bisa zarginsa da aikata laifuka 14 da suka hada da satar N11, 498, 944, 038.29 mallakin 'First Bank Plc'.

- Daga karshe mai shari'ar, Dada, ya tabbatar da samun wanda ake zargin da aikata dukkanin laifukan da ake tuhumarsa, inda ya yanke masa shekara daya a gidan wakafi

A ranar Laraba, hukumar da ke yaki da masu yiwa dukiyar jama'a zagon kasa da kuma cin hanci da rashawa EFCC ta mika motoci 116 da gidaje 20 a jihohin Edo, Rivers da Legas da ta kwato daga hannun wani mutumi mai suna Michael Obasuyi ga 'First Bank Plc.'

Rikicin dai ya fara ne tun lokacin da Osasogie ya rubuta takardar korafi ga hukumar akan kamfanin E-tranzact a watan Maris 2018.

Sai dai, EFCC, ta binciki ribar da Osasogie ke samu a kasuwancinsa, bayan da shima kamfanin E-tranzact ya rubuta takardar korafi ga hukumar kan Osasogie da wani kamfaninsa mai suna, SmartMicro.

Rahotanni sun bayyana cewa kamfanin SmartMicro a 2016 ya bukaci kamfanin E-tranzact da su kulla yarjejeniyar hannun jari mai suna "Corporatepay" don biyan albashin ma'aikatan jihar Delta a bankunan yan kasuwa.

KARANTA WANNAN: Gwamnatin Buhari ta sankame asusun bankunan wadanda suka yi badakala da dukiyar kasa

Daga karshe: EFCC ta mikawa 'First Bank' motoci 116 da gidaje 20

Daga karshe: EFCC ta mikawa 'First Bank' motoci 116 da gidaje 20
Source: Twitter

Sai dai, E-tranzact yayi ikirarin cewa a watan Maris 2018, ya gano cewa bankin na SmartMicro ya ci bashi tsundum har na N11, 498,944,038.29.

Obasuyi, a cikin wata sanarwa da ya aikewa hukumar EFCC, ya amince da aikata wannan laifi da ake zarginsa, yana mai bayyana cewa ya kirki kudaden jabu ta tallafin wata manhaja ta "Fundgate Financial" wacce ya samu daga kamfanin.

Haka zalika, an gurfanar da Osasogie tare da wasu kamfanoninsa na "Platinum Multi-Purpose Co-operative Society, SmartMicro Systems Limited da kuma Platinum Smart Cruise Motors Limited" a 24 ga watan Mayu 2018, a gaban mai shari'a Mojisola Dada na kotu ta musamman da ke duba kararraki na musamman da ke zama a Ikeja, bisa zarginsa da aikata laifuka 14 da suka hada da satar N11, 498, 944, 038.29 mallakin 'First Bank Plc'.

DUBA WANNAN: EFCC: Kotun daukaka kara ta garkame shugaban hukumar SUBEB shekaru 41 a gidan kaso

Ba tare da wahalar da shari'a ba, ya amince da wannan zargi da ake masa.

Hukumar EFCC ta gano N2, 903,727,563.92, $37, 992.87 da kuma €18,538.09 a asusun bankuna dabn daban mallakin Osasogie, haka zalika hukumar ta kwato motoci 116 da gidaje 20 a jihar Legas, Abuja, Benin da Fatakwal mallakinsa.

Daga karshe mai shari'ar, Dada, ya tabbatar da samun wanda ake zargin da aikata dukkanin laifukan da ake tuhumarsa, inda ya yanke masa shekara daya a gidan wakafi, haka zalika ya baiwa hukumar EFCC umurnin mayarwa 'First Bank Plc' gidaje 20 da motoci 116 da aka kwato daga Osasogie.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Mailfire view pixel