Masha Allah: An rantsar da sabbin lauyoyi 4,779 a Nigeria

Masha Allah: An rantsar da sabbin lauyoyi 4,779 a Nigeria

- A ranar Laraba aka kammala rantsar da daliban da suka kammala karatu a fannin lauyanci guda 4,779 a matsayin cikakkun lauyoyi

- Sai dai kwamitin ladabtarwa na lauyoyi, tsakanin watan Janairu zuwa Nuwamba ya kwace lasisin aikin lauyoyi 7 bisa aikata laifuka daban daban

- A nashi bangaren, Farfesa Isa Hayatu Chiroma (SAN), ya ce daga cikin dalibai 161 da suka kammala makarantar da matakin (first class), 133 mata ne, sai maza 48

A ranar Laraba aka kammala rantsar da daliban da suka kammala karatu a fannin lauyanci guda 4,779 a matsayin cikakkun lauyoyi.

Shugaban hukumar da ke tabbatar da daliban da suka kammala karatun lauyanci ta kasa, (BOB), Alhaji Bashir Dalhatu, ya sanar da hakan a lokacin tantance daliban da kuma rantsar da su, inda kuma ya bayyana cewa kwamitin ladabtarwa na lauyoyi, tsakanin watan Janairu zuwa Nuwambar wannan shekarar, ya kwace lasisin aikin lauyoyi 7 bisa aikata laifuka daban daban da sukabawa aikin lauyanci.

Dalhatu ya kuma ce an dakatar da lauyoyi 12, yayin da kwamitin ya gargadi wani lauya guda daya, bisa aikata laifuka daban daban da suka saba da ka'idar gudanar da aikin lauyanci.

Ya ce, sabbin lauyoyi 4,779 da aka rantsar da su, sun tsallake jarabawar karshe ta zangon Ogusta/Satumba 2018

KARANTA WANNAN: Daga karshe: Rundunar 'yan sanda ta kori jami'inta da ya kashe wani dalibin jami'a

Masha Allah: An rantsar da sabbin lauyoyi 4,779 a Nigeria

Masha Allah: An rantsar da sabbin lauyoyi 4,779 a Nigeria
Source: Depositphotos

Dalhatu ya ce kwamitin na LPDC, wacce wani sashe ne na hukumar BOB, ta kasance tana gudanar da ayyukanta cikin adalci ba tare da nuna banbanci ko son kai ba.

Ya shawarci sabbin lauyoyin da su kasance masu nuna halaye nagari da kuma bin dokoki da tsare tsaren da ke kunshe a cikin kundin tsarin aikin lauyanci.

A nashi bangaren, babban daraktan makarantar lauyanci ta Nigeria, Farfesa Isa Hayatu Chiroma (SAN), ya ce a karon farko na tarihin makarantar, an samu dalibai 161 da suka zarce jami'o'i 15, da suka kammala da matakin farko na sakamako (first class).

Ya ce daga cikin dalibai 161 da suka kammala da sakamako na matakin farko, 133 daga cikinsu mata ne, yayin da 48 suka kasance maza.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel