An cire Buhari da Atiku daga tattaunawar shugabannin Kiristoci

An cire Buhari da Atiku daga tattaunawar shugabannin Kiristoci

Wata kungiyar shugabannin Kirista sun cire dan takarar shugaban kasa a APC, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da na PDP, Atiku Abubakar daga wani taron tattaunawa da yan takarar shugabancin kasa.

Shugabannin kungiyar mai suna Christian Elders Forum (NCEF), sunce an cire Atiku da Buhari ne saboda jam’iyyar a suke ta PDP da APC, wadanda suke jefa kasar cikin kangi na talauci a duniya, jaridar Punch ta ruwaito.

Bosun Emmanuel, sakataren kungiyar a wata sanarwa ya bayyana yan takarar shugaban kasar da za’a gayyata wajen taron da suransu wadanda ba yan APC da PDP bane.

An cire Buhari da Atiku daga tattaunawar shugabannin Kiristoci

An cire Buhari da Atiku daga tattaunawar shugabannin Kiristoci
Source: Depositphotos

Kungiyar ta shawarci yan Najeriya da su marawa sabbin yan takara baya a matsayin zabinsu a zaben 2019.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa ta tabbatar da zabin Buhari a matsayin sakataren EFCC

Vanguard ta ruwaito cewa kungiyar tabayyana cewar za ta yi taron ne aranar Juma’a, 30 ga watan Nuwamba, a Onigbagbo House, Mobolaji Bank Anthony Way, Ikeja jihar Lagas da karfe 12 na rana.

Manyan jam’yyar sun hada Solomon Asemota, Tsohon ministan tsaro Janar Theophilus Danjuma, Joseph Otubu, Joshua Dogonyaro, Archbishop Magnus Atilade, Kate Okpareke, Ayo Abifarin, Zamani Lekwot, Moses Ihonde, Nat Okoro, Matthew Owojaiye da sauransu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel