Na roke su (Ja’afar Ja’afar) kada su saki bidiyon amma basu saurareni ba - Kwankwaso (kalli bidiyo)
Sanata mai wakiltan mazabar Kano ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa yana sane da bidiyon da ke nuna gwamnan jihar , Abdullahi Umar Ganduje, yana karban kudi daga hannun yan kwangila.
Ya bayyana cewa ya yi iyakan kokarinsa wajen ganin cewa kada a saki bidiyon nan amma abin bai yiwu ba.
Kana ya bayyana cewa karya akayiwa shugaba Muhammadu Buhari cewa ya karkatar da kudin jihar Kano wajen yakin neman zaben shugaban kasa. Da kuma cewa Ganduje ne ya karasa ayyukan da ya bari.
KU KARANTA: Babbar magana: Na kashe budurwata saboda tana soyayya da yayana - Dan shekaru 16
Kwankwaso, wanda tsohon gwamna ne a jihar Kano, ya bayyana wadannan kalamai ne yayinda yake hira a tashar rediyon Aminchi FM.
Sanata Kwankwaso ya ce ya roki shugaban jaridar yanar gizon, Daily Nigerian, da ya saki bidiyon amma basu sauraresa ba.
Yace: “Ina sane da bidiyon kafin a sakewa duniya ta gani kuma na rokesu kada su saki, amma basu saurareni ba.”
Kalli wani ballin bidiyon jawabinsa:
Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng
Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng