Babbar magana: Na kashe budurwata saboda tana soyayya da yayana - Dan shekaru 16

Babbar magana: Na kashe budurwata saboda tana soyayya da yayana - Dan shekaru 16

- Rundunar 'yan sanda ta cafke Idrisu Muhammadu bisa zarginsa da kashe budurwarsa mai suna Fatima Isah saboda tana soyayya da yayansa

- A shekaru 3 da suka wuce, Muhammadu ya taba yin barazanar kashe Fatima ma damar ba shine ya aureta ba, barazanar da har mahaifinta ya sana da 'yan sanda

- Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sanda na jihar Niger, Mohammad Abubakar, ya ce Idrisu ya amince da wannan zargi na kashe Fatima da adda

Rundunar 'yan sanda ta samu nasarar cafke Idrisu Muhammadu dake zaune a kauyen Evutagi, karamar hukumar Katcha, jihar Niger, bisa zarginsa da kashe budurwarsa mai suna Fatima Isah, wacce take zaune a gari daya da Muhammadu.

An yi zargin cewa Muhammadu ya kashe budurwarsa saboda tana soyayya da yayansa.

Rahotanni sun bayyana cewa, wanda ake zargin, ya kashe tsohuwar budurwarsa, bayan da mahaifinta, Isah Evutagi, ya yanke hukuncin aurar da diyarsa ga wani mutumin daban ba Idrisu ba.

KARANTA WANNAN: 2019: Atiku, shuwagabannin PDP sun ziyarci Ekweremadu, sun zayyana dalilin zabar Obi

Babbar magana: Na kashe budurwata saboda tana soyayya da yayana - Dan shekaru 16
Babbar magana: Na kashe budurwata saboda tana soyayya da yayana - Dan shekaru 16
Asali: Facebook

Shafin jaridar Nothern City ta tattara rahoton cewa, tun a baya Muhammadu ya yi ikirarin cewa zai kashe Fatima ma damar ba shine ya aureta ba. Haka zalika, mahaifin mamaciyar, ya kai karar wannan barazana da Muhammadu ya yi ga rundunar 'yan sanda, tun shekaru 3 da suka gabata.

Wanda ake zargin ya shaidawa manema labarai cewa shi da yayansu, suna soyayya da Fatima, tare da cewa "Na gayawa yayana ya bar min Fatima saboda na shirya aurenta, amma baiji maganata ba, ya ci gaba da zuwa wajenta, har sai da ya kaini makura, na kashe ta.

"Ku kalli yadda taurin kunnensa ya haddasa; yanzu na zama mai kashe mutane. Zan kare rayuwata gaba daya a gidan yari, tun ina da shekaru 16; kaico na!"

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sanda na jihar Niger, Mohammad Abubakar, ya ce wanda ake zargin ya amince da wannan zargi da ake masa na kashe budurwarsa da adda, yana mai cewa dama dai tun a baya yayi ikirarin kashe ta idan har yayansa bai daina zuwa wajenta ba.

Mai magana da yawun rundunar ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu da zaran rundunar ta kammala bincike akansa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel