NDLEA ta kama jami’an yan sanda 2 da ke yi ma alburusai 1,250 rakiya

NDLEA ta kama jami’an yan sanda 2 da ke yi ma alburusai 1,250 rakiya

Hukumar kula da hana safarar miyagun kwayoyi (NDLEA) ta sanar da cewa jami’anta sun kama wasu jami’an yan sandan Najeriya biyu kan zargin kasancewarsu da hannu a waen shigo da alburusai 1,250.

Kakakin hukumar ta NDLEA, Jonah Achema, a wani jawabi a ranar Talata, 2 ga watan Nuwamba ya ce hukumar reshen Abuja c eta kama alburusan a lokacin wani rangai a yankin Gwagwalada da ke a hanyar babbar titin Abuja-Lokoja.

A cewar sanarwar, an tura makama ne ta kamfanin sufuri daga Lagas inda yan sandan za su karba.

NDLEA ta kama jami’an yan sanda 2 da ke yi ma alburusai 1,250 rakiya
NDLEA ta kama jami’an yan sanda 2 da ke yi ma alburusai 1,250 rakiya
Asali: Twitter

Achema ya ce an kama yan sandan subiyu bayan dukkaninsu sun yi ikirarin mallakar sakon. Yace an tura wadanda ake zargin da kayayyakin ga hukumar yan sanda.

KU KARANTA KUMA: Rundunar Sojin Najeriya ta dakile harin 'yan Boko Haram

A watan Oktoba, 2018, Legit.ng ta rahoto yadda yan sandan Najeriya suka kama wani mutum dan shekara 43 da yayi wa hukumar EFCC sojan gona don ya damfari wani kamfani.

Nigerian Tribune ta rahoto cewa wani mutum kuma mai shekara 42, Sodiq Inusa wanda ya dade yana yiwa yan sanda sojan kona ya shiga hannu sannan kuma an kwace indigar da yake aiki dashi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng