Ba zan hana kowa barin APC ba, kowa na da 'yancin bin ra'ayinsa - Gwamna Okorocha

Ba zan hana kowa barin APC ba, kowa na da 'yancin bin ra'ayinsa - Gwamna Okorocha

- Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya bude kofa ga duk wani dan takara da yake ganin APC bata yi masa adalci a zaben fidda gwani ba, da ya bar jam'iyyar

- Okorocha wanda ya ce zai ci gaba da tsaya a APC don yin takarar kujerar Sanata, ya ce zai goyi bayan 'yan takarar a kowacce jam'iyya suka koma

- Ya kuma bayyana Sanata Hope Uzodinma da APC ta gabatar da sunan a matsayin dan takarar gwamnan jihar, a matsayin cin fuskar siyasa mafi muni a tarihin siyasar Nigeria

A ranar Talata, gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha ya bude kofa ga tsohon shugaban ma'aikatansa, Uche Nwosu, wanda shima yake takarar kujerar gwamnan jihar, da ma duk wani dan takara da yake ganin ba ayi masa dai-dai a zaben fitar da gwani na APC da ya gudana a jihar ba, da ya ficve daga jam'iyyar zuwa wata, don cimma muradun zuciyarsa, a cewarsa, ba zai dakatar da kowa ba.

Rahoton da Legit.ng ta tattara, ya bayyana cewa sama da mambobi 27 a majalisar dokoki ta jihar da kuma majalisun tarayya, da suka hada da Nwosu, wadanda suke ganin APC bata yi masu adalci ba a zabukan fitar da gwani, na shirin sauya sheka zuwa wata jam'iyyar kafin a rufe kofar sauya sunayen 'yan takara.

KARANTA WANNAN: APC: Yan Nigeria na jiran 2019 don sakawa Buhari da alkairi

Ba zan hana kowa barin APC ba, kowa na da 'yancin bin ra'ayinsa - Gwamna Okorocha
Ba zan hana kowa barin APC ba, kowa na da 'yancin bin ra'ayinsa - Gwamna Okorocha
Asali: Depositphotos

Okorocha ya jaddada cewa, shi zai ci gaba da zama a cikin APC, kuma zai tsaya takarar mazabar Orlu a majalisar dattijai karkashin jam'iyyar, haka zalika ya tabbatar masu cewa zai goyi bayansu a duk inda suke.

Sai dai, gwamnan ya jaddada cewa 'yan takarar da ke fushi da jam'iyyar sune zabinsa, kuma zai ci gaba da basu duk wata gudunmowa da suke bukata, karkashin kowacce jam'iyya suka koma don cimma muradunsu na siyasa.

Da yake jawabi ga manema labarai a Owerri, Okorocha ya jaddada cewa, Nwosu, a kowacce jam'iyya ya koma, zai ci gaba da kasancewa dan takararsa na gwamnan jihar, yana mai bayyana Sanata Hope Uzodinma da APC ta gabatar da sunan a matsayin cin fuskar siyasa mafi muni a tarihin siyasar Nigeria.

Okorocha ya bayyana takaicin sa kan cewa an kakabawa al'ummar jihar Imo, 'yan takarar da basu so a manyan jam'iyyun siyasar jihar; APC, PDP, da APGA, yana mai cewa dukkanin 'yan takara karkashin jam'iyyar, ba zabin jama'a bane, tilastawa ce kawai.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng