Yan ta’addan Boko Haram sun kashe manoma 4 a Maiduguri

Yan ta’addan Boko Haram sun kashe manoma 4 a Maiduguri

Kasa da mako guda bayan mambobin kungiyar yan ta’addan Boko Haram sun kashe sojoji a Matele, an rahoto cewa gamayyar Abubakar Shekau na kungiyar sun kuma kashe wasu manoma hudu a Jiddari-Polo, kusa da Maiduguri, jihar Borno.

An rahoto cewa maharani sun kai mamaya garin ne a kafa, inda suka raunata wani manoni sannan suka kale wani manomi dan shekara 75, Mala Umara, dauke da sakon cewa sojojin da ke girke a Jiddari-Polo da su sammaci mumunan hari.

Umara yace: “Sun zo su da yawa a kafa yayinda muke gona sannan suka kamamu mu shida inda sauran suka tsere.

Yan ta’addan Boko Haram sun kashe manoma 4 a Maiduguri
Yan ta’addan Boko Haram sun kashe manoma 4 a Maiduguri
Asali: Depositphotos

“Sun kashe hudu a kan idanuna sannan suka bar mutun guda da mumunan rauni.

“Sun bukaci da na isar da sakonsu ga sojoji cewa su shirya ma wani hari kwanan nan. Sun fada mun sakon har sau uku inda suka jadadda cewa na isar dashi ga sojoji.”

Wani manomi, Abba Muhammad wanda ya sha da kyar lokacin da maharani suka kai mamaya gonar, yace yan bindigan sun tambaye shi sansanin sojoji a Jiddari-Polo.

KU KARANTA KUMA: 2019: Tazarce na kamar anyi an gama ne – Gwamna El-Rufai

Yace: “Su biyar dauke da makamai da bindigu sun tare ni sannan suka fara tambaya na inda sojoji suke a Jiddari-Polo.

“Daya daga cikinsu yayi ihun cewa su far mun da adda amma a take na ci na kare. Su biyu sun bi ni amma na fi su sauri. Sun dauke keke na.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng