Ba kunya ba tsoron Allah: Fadar shugaban kasa ta tsulawa 'yan Najeriya karya
- Wani bincike ya kabo jirgin karyar fadar shugaban kasar Najeriya
- Fadar shugaban kasa ta tsulawa 'yan Najeriya karya
Mai baiwa shugaban kasa, Muhammadu Buhari shawara na musamman akan harkokin yada labarai, Mista Femi Adesina a cikin wata fira da yayi da manema labarai ya bayyana cewa sojojin kasashe a duk inda suke basa fadar irin asarar rayukan da suka samu.

Asali: Depositphotos
KU KARANTA: Ina cikin masoyan Buhari na zahiri - Kwankwaso
Sai dai wani bincike da masana da sauran 'yan Najeriya da ma 'yan jarida ya gano cewa maganar ta sa ba akan gaskiya take ba domin kuwa ba haka abun yake ba a kasashen da suka cigaba.
Legit.ng Hausa ta samu cewa wannan muhawarar na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta cece-kuce game da ainihin adadin yawan sojojin da 'yan ta'addan Boko Haram suka kashewa Najeriya biyo bayan artabun da sukayi da su a satin da ya gabata.
Yayin da kafofin yada labarai a Najeriya din suka ce yawan sojojin sun kai 157, bangaren gwamnati sun karyata alkaluman duk kuwa da cewa su basu bayar da nasu alkaluman ba.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng