A hakikanin gaskiya ba bu mai son Buhari kamar ni - Kwankwaso

A hakikanin gaskiya ba bu mai son Buhari kamar ni - Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano, kuma Sanata mai wakiltar shiyyar jihar ta tsakiya, Sanata Rabi'u Kwankwaso, ya ce shi ba zai mayar wa da shugaban kasa Muhammadu Buhari martani ba a kan zargin da ya yi nasa na cewa ya kwashe kudin jihar ya yi yakin neman zabe a shekarar 2015.

Sanata Kwankwaso ya ce dalilin kuwa da ba zai ce komai ba akan hakan shine saboda shugaban kasar bai san komai a kan siyasar jihar ta Kano da kuma yarda ya tafiyar da mulkin sa sadda yana bisa kujera.

A hakikanin gaskiya ba bu mai son Buhari kamar ni - Kwankwaso
A hakikanin gaskiya ba bu mai son Buhari kamar ni - Kwankwaso
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Masana sun gano maganin tsufa

Haka ma dai Sanatan kuma jagoran darikar siyasa ta Kwankwasiyya ya ce wasu mutanen dake zagaye da Shugaba Buhari sun je suna gaya masa cewa shi dan ta'adda ne, ba ya son Buhari amma alhalin a hakikanin gaskiya duk cikin wadannan mutane ba wanda yake son Buhari kamar shi domin shi ne ya taimake shi ya ci zabe.

Legit.ng Hausa ta samu cewa dan majalisar dattawan ya bayyana hakan ne a wata hira ta musamman da aka yi da shi a gidan rediyon Dala FM da ke jihar ta Kano ranar Talata da daddare.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a kwanan baya ne lokacin da Shugaba Buhari ke ziyarar aiki a kasar Faransa, ya shaida wa wani taron 'yan Najeriya, ciki har da 'yan jihar Kano, cewa gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya kammala ayyukan da mutumin da ya gada, Sanata Kwankwaso ya bari bayan da ya kwashe kudin jihar ya yi yakin neman zaben shugaban kasa a 2015.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel