Ba ni na zabi mahaifina ba - Diyar Abacha, Gumsu

Ba ni na zabi mahaifina ba - Diyar Abacha, Gumsu

Fatima Gumsu, diyar tsohon shugaban kasar Najeriya a mulkin soji, Janar Sani Abacha, ta bayyana cewar ba ita ce ta zabi Abacha ya zama mahaifinta ba.

Gumsu ta yi wannan kalami ne bayan shan suka a kan yadda mahaifinta ya yi kwashi dukiyar Najeriya lokacin mulkinsa.

Wani dan Najeriya ma'abocin bibiyar shafin sada zumunta ne ya soki Gumsu, a shafin sada zumunta, kan cewar basu san matsalar Najeriya ba saboda an haife su cikin daula.

Ba ni na zabi mahaifina ba - Diyar Abacha, Gumsu
Ba ni na zabi mahaifina ba - Diyar Abacha, Gumsu
Asali: Twitter

Ita kuma Gumsu a nata martanin sai ta ce; "ba ni na zabi waye zai zama mahaifina ba."

DUBA WANNAN: Gwamna Yari ya dakatar da sarakuna hudu a Zamfara

An zargi Marigayi Abacha da kwasar makudan kudin Najeriya tare da jibge su a asusun 'ya'yansa a bankunan kasashen ketare, musamman kasar Switzerland dake nahiyar Turai.

Tun bayan rasuwar sa gwamnatocin bayansa ke karbo irin kudaden da Abacha ya kai asusun ajiyar 'ya'yansa a bankunan Switzerland.

Hatta wannan gwamnatin ta shugaba Buhari ta karbo irin wadannan kudade kuma da su ne yanzu take daukan nauyin shirin tallafawa kananan 'yan kasuwa da jari a karkashin wani shiri mai taken "Trader Moni".

Batun kwasar makudan kudade a wurin shugabannin Najeriya da na wasu kasashen nahiyar Afrika ba bakon abu ne. Hakan na daga cikin matsalolin da su ka sa kasashen Afrika ke fama da matsanancin talauci da kuma jawowa yankin rashin kima a idon ragowar kasashen duniya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng