Kisan sojoji: Buhari zai tafi Maiduguri ranan Laraba
Shugaba Muhammadu Buhari ya fasa tafiya jihar Edo ranan Talata inda yayi niyyar halartan taron babban hafsan hukumar sojin kasa da aka shirya a birnin Benin. Saboda haka, an mayar da taron jihar Borno.
Hadimin shugaban kasa kan sabbin kafafen yada labarai, Bashir Ahmad, ya tabbatar da wannan labari inda yace: “Shugaba Muhammadu Buhari zai kaddamar da taron COAC a ranan 28 ga watan Nuwamba, 2018 a farfajiyar taro a Maiduguri, jihar Borno.”
“Da farko an shirya taron ne daga ranan 26 zuwa 28 a birnin Benin, jihar Edo.”
Gabanin wannan canjin tsari, an shirya shugaba Buhari zai kaddamar da kamfanin wutan lantarki na Edo-Azura a ranan 27 ga watan Nuwamba, 2018.”

Asali: UGC
An tattaro cewa an canza wajen taron ne sakamakon kisan sojoji da yan Boko Haram sukayi a makon da ya gabata, a garin Matele, wani kauye tsakanin Najeriya da Chadi.
Kana an samu labarin cewa shugaba na son amfani da wannan dama wajen tattaunawa da sojojin da ke filin daga.
KU KARANTA: Buhari ya watsawa Oshiomole kasa a ido, ya yi watsi da barazanar da APC ta yiwa mambobi
Mun kawo muku rahoton cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya shiga ganawar gaggawa da manyan hafsoshin tsaron Najeriya a fadar shugaban kasa, Aso Villa yanzu. Jaridar Daily Trust ta bada rahoto.
Babban mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Babagana Munguni da sifeto janar na hukumar yan sanda, Ibrahim Idrs, sun isa fadar shugaban kasa ne misalin karfe 2:50 na rana.
Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng