Za’a iya magance matsalolin Najeriya ta hanyar addu’a – Yakubu Gowon

Za’a iya magance matsalolin Najeriya ta hanyar addu’a – Yakubu Gowon

- Yakubu Gowon, tsohon shugaban Najeriya ya ce ya zama dole coci su dunga nusar da mabiyansu kyawawan halayya da tsoron Allah

- Gowon ya bayyana cewa za’a iya magance matsalolin Najeriya ta hanyar dagewa da addu’a a coci, maimaikon tayar da rikici, ramuwar gayya da kuma rashin yafiya

- Ya ce Allah ne maganin matsalolin Najeriya amma ba wai bindiga da ramuwar gayya ba

Tsohon shugaban kasa, Yakubu Gowon, a ranar Lahadi, 25 ga watan Nwamba ya udanar da wani taron addu’a domin Najeriya a hedkwatar Deeper Life Bible Church da ke Lagas.

Gowon ya bayyana cewa za’a iya magance matsalolin Najeriya ta hanyar dagewa da addu’a a coci, maimaikon tayar da rikici, ramuwar gayya da kuma rashin yafiya.

Tsohon shugaban kasar wanda ya jagoranci yiwa kasar Najeriya addu’a, ya kasance tare da mai masaukin baki, Fasto Kumyi, babban faston Deeper Christian Life Ministry da matarsa, Fasto Esther.

Za’a iya magance matsalolin Najeriya ta hanyar addu’a – Yakubu Gowon
Za’a iya magance matsalolin Najeriya ta hanyar addu’a – Yakubu Gowon
Asali: Depositphotos

Taron na shekara-shekara ya tara manyan kiristoci daga dariku daban-daban da kuma manyan yan siyasa da ke rike da mukaman gwamnati.

Gowon ya bukaci da a taru a yiwa kasar addu’a, cewa Allah na tare da halin da Najeriya ke ciki a koda yaushe, kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito.

KU KARANTA KUMA: 2019: Gwamnoni da 'yan majalisar APC a jihohin arewa 6 sun yi taro a kan Atiku

A cewarsa, al’umman kasa za su taka gagarumin rawar gani ta hanyar ci gaba da wanzar da zaman lafiya da hadin kai domin ci gaban Najeriya.

Ya kuma kalubalanci mabiya addinin Kirista da guje ma ramuwar gayya, rikicin addini da sauran ayyukan assha.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng