EFCC ta samu takardar hurumin kudunduno tsohuwar ministar mai, Diezani zuwa Najeriya
Hukumar nan ta gwamnatin tarayya dake yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) ta samu takardar hurumin kamo tsohuwar ministar mai ta Najeriya, Diezani Alison Madueke zuwa Najeriya.
Haka zalika mun samu cewa hukumar ta Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) ta yi kari akan wasu tuhume-tuhumen da suke yi mata a kotun wanda zai bata damar kudunduno tsohuwar ministar ya zuwa Najeriya.

Asali: Depositphotos
KU KARANTA: Wani saurayi ya guntule hannun abokin hamayyar sa a Adamawa
Legit.ng Hausa dai ta samu cewa tsohuwar ministar tun bayan faduwar gwamnatin Jonathan zabe a shekarar 2015, ta tsere ya zuwa kasar Birtaniya inda take neman mafaka akan zarge-zargen da ake yi mana na almundahana da dukiyar al'umma.
A wani labarin kuma, Rundunar sojin Najeriya ta sanar da hannan ta wasu tubabbun manyan mayakan 'yan ta'addan Boko Haram akalla 155 zuwa ga gwamnatocin jahohin Borno, Yobe da kuma Adamawa domin mayar da su cikin iyalan su.
Shugaban shirin rundunar sojin na horarwa tare da sake tsugunnar da 'yan ta'addan Manjo Janar Bamidele Shafa shine ya sanar da hakan lokacin da yake jawabi a wajen bikin mika tubabbun 'yan ta'addan a garin Gombe.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng