Rikicin APC: Za muyi anfani da tsala-tsalan mata wajen ban hakuri ga wadanda suka hasala - Oshiomhole

Rikicin APC: Za muyi anfani da tsala-tsalan mata wajen ban hakuri ga wadanda suka hasala - Oshiomhole

Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a mataki na kasa, Kwamared Adams Oshiomhole ya ce za suyi anfani da mata wadan da suka ansa sunan su wajen karkato da zukatan wadanda aka batawa rai a jam'iyyar.

Mista Oshiomhole ya bayyana hakan ne a yayin da yake jawabi a wajen kaddamar da kwamitocin da jam'iyyar ta kafa har guda shidda don sasanci da kuma shawo kan 'ya'yan jam'iyyar da ke rikici da junan su.

Rikicin APC: Za muyi anfani da tsala-tsalan mata wajen ban hakuri ga wadanda suka hasala - Oshiomhole
Rikicin APC: Za muyi anfani da tsala-tsalan mata wajen ban hakuri ga wadanda suka hasala - Oshiomhole
Source: UGC

KU KARANTA: Wani mutum ya kashe budurwar sa yayi balangu da ita

Legit.ng Hausa ta kuma tsinkayi Adams Oshiomhole din yana cewa za suyi hakan ne domin a cewar sa su Allah ya basu wata irin baiwar lallashi da iya kalallame mutum da dadin baki.

A wani labarin kuma, A halin yanzu dai rikicin cikin gida a tsakanin 'ya'yan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a jihar Nasarawa dake a yankin Arewa ta tsakiya ya kara kamari yayin da ake tunkarar zabukan shekarar 2019.

Kamar dai yadda muka samu, bangarorin dake rikici da juna da suka hada da na gwamnati karkashin jagorancin gwamnan jihar da kuma na Sanata Abdullahi Adamu da Ahmed Wadada sun kara farraka kan 'ya'yan jam'iyyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng