Ba lafiya: An tsinci gawa ba kai da wasu sassan jiki a wata jiha a Najeriya

Ba lafiya: An tsinci gawa ba kai da wasu sassan jiki a wata jiha a Najeriya

Gawar wata mata da aka tsinta ba kai a wani unguwa a garin Enugu ya razanar Al’umma mazauna wata unguwa a garin Enugu, babban birnin jihar ta Enugu dake a shiyyar kudu maso gabashin Najeriya.

Kafar sadarwa na zamani mai suna ‘Laila Blog’ ne ta fara watsa labarin gawar matar, inda ta nuna hotunan gawar matar yayin da jami’an rundunar yansanda ke tafiya da gawar a ranar Larabar daga gabata.

Ba lafiya: An tsinci gawa ba kai da wasu sassan jiki a wata jiha a Najeriya
Ba lafiya: An tsinci gawa ba kai da wasu sassan jiki a wata jiha a Najeriya
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yadda yan Boko Haram suka yi fata-fata da sojin Najeriya

Sai dai har zuwa lokacin hada wannan labarin, ba’a san takamaimen wace mata ce wannan ba, sai dai sakamakon an yanke mata kai, jama’ar yankin na ganin kamar yan kungiyar matsafa ne suka aikata mata wannan mummunar aika aika.

A wani labarin kuma an kama wasu masu satar mutane a yankin Epe na jihar Legas yayin da suke kokarin tserewa. Jama’an unguwar Epe ne suka kama barayin, inda suka yi musu tsirara sa’annan suka jibge su kamar kayan wanki.

Daga bisani wasu mutane da suka harzuka sun bukaci da a babbaka barayin, sai dai bamu samu tabbacin ingantaccen labarin cewa an babbaka su ba ko a’a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng