Kishi kumallon 'maza': Wani saurayi ya guntule hannun abokin hamayyar sa kan budurwa a Yola

Kishi kumallon 'maza': Wani saurayi ya guntule hannun abokin hamayyar sa kan budurwa a Yola

Jami'an 'yan sandan Najeriya shiyyar jihar Adamawa sun tabbatar da cafke wani saurayi mai suna Abubakar Yahaya da tsananin kishi ya sa ya guntulewa abokin hamayyara sa mai suna Mohammed Jafar hannu akan budurwa.

Mai magana da yawun rundunar ta 'yan sandan jihar Othman Abubakar shine ya bayyawa manema labarai hakan a hedikwatar su dake a garin Jimeta, Yola.

Kishi kumallon 'maza': Wani saurayi ya guntule hannun abokin hamayyar sa kan budurwa a Yola
Kishi kumallon 'maza': Wani saurayi ya guntule hannun abokin hamayyar sa kan budurwa a Yola
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: An kama wani malamin addini da matar aure

Legit.ng Hausa ta samu cewa matasan sun tafka kazamin fada ne akan budurwar tasu mai suna Mariam Boni inda anan ne shi Abubakar din ya samu sa'ar abokin hamayyar sa ya ya sare masa hannu da adda wanda yanzu haka yana a asibiti yana karbar kulawar likita.

A wani labarin kuma, Wasu rahotannin da muke samu marasa dadin ji daga jihar Borno a Najeriya na cewa mayaka da ake zaton 'yan Boko Haram ne sun sace mutane fiye da hamsin a yankin Gamborou kusa da iyaka da Kamaru.

Maharan dai kamar yadda muka samu sun kewaye mutanen ne a lokacin da suka je daji yin itacen hura wuta amma suka yi anfani da rashin tsaron dake a yankin suka yi awon gaba da su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng