Cike da alhini: Rundunar soji ta kwaso gawarwakin sojoji 70 da Boko Haram ta kashe a Metele
- Rundunar soji a Maiduguri ta kwaso gawarwakin jami'an sojin da mayakan Boko Haram suka kashe a ranar Lahadi a kauyen Metele, jihar Borno
- A cewar wata majiya, an kwaso gawarwakon sojoji 70, yayin da sama da sojoji 100 ne ake sa ran sun mutu a wannan harin na kauyen Metele
- Duk wani yunkuri na zantawa da mai magana da yawun rundunar soji, Birgediya Janar Chukwu Texas don yin tsokaci kan wannan rahoto yaci tura
Rahotannin da muka samu, daga shafin jaridar The Nation na nuni da cewa, rundunar soji a Maiduguri ta kwaso gawarwakin jami'an sojin da mayakan Boko Haram suka kashe a ranar Lahadi a kauyen Metele, karamar hukumar Guzamala da ke Arewacin jihar Borno.
Wata majiya da ta zanta da jaridar The Nation, ta bayyana cewa sama da gawarwakin sojoji 70 ne aka kwaso zuwa Maiduguri bayan da sashen shirin Operation Lafiya Dole na rundunar a jihar da kuma rundunar GOC ta 7, suka isa Monguno don tsara yadda zasu kwaso gawarwakin sojojin da aka kashe.
Majiyar ta kara da cewa sama da sojoji 100 ne ake sa ran sun mutu a wannan harin na kauyen Metele.
KARANTA WANNAN: Yahoo Yahoo: A police force kidnapped those who killed Delta University student

Asali: Facebook
Haka zalika, jaridar The Nation ta ruwaito cewa kashin farko na tawagar kai daukin gaggawa da kwaso matattun sun kasa isa wajen, sakamakon wani harin da mayakan Boko Haram suka sake kaiwa a sansanin sojin, wanda ya tilastasu hakura da kai agajin.
"Zuwa yau, an kawo gawarwakin sojoji sama da 70 nan Maiduguri. Sai dai na tabbatar akwai sauran sojojin da zai yi wuya a gano su. Ba ni da tabbas amma ina da yakinin cewa sojojin da suka mutu a wannan harin sun haura 100," a cewar majiyar.
Wani soja da ya tsallake rijiya ta baya baya a harin da aka kai, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya kara bayyana cewa mayakan da suka kaddamar da harin, sun isa sansanin sojin ne cikin lumana a matsayin masu kawo dauki, har suka shiga ofishin kwamandan rundunar, inda nan take suka harbe shi da wasu sojoji 5 da ke tare da shi a cikin ofishin.
KARANTA WANNAN: Buhari ya sha alwashin karya farashin magunguna a Nigeria
A cewar majiyar, sojojin da ke a waje sai suka cika da mamaki jiyo karar harbe harben bindiga daga cikin ofishin kwamandan nasu. Sai dai kafin suyi wani yunkuri, mayakan Boko Haram ta kowanne bangare sun mamaye sansanin tare da bude masu wuta.
Idan ba a manta ba a baya baya, wasu dakarun soji a Metele sun taba fuskantar makamancin wannan harin a watan Satumbar wannan shekarar, inda sojoji akalla 18 suka mutu yayon da aka nemi sojoji 151 ciki harda manyan jami'an soji 6, aka rasa su ko sama ko kasa, kuma a yankin ne aka kaiwa bataliya ta 157 hari a 8 ga watan Oktobar wannan shekarar.
Duk wani yunkuri da jaridar The Nation tayi na zantawa da mai magana da yawun rundunar soji, Birgediya Janar Chukwu Texas don yin tsokaci kan wannan rahoto yaci tura sakamakon rashin amsa kiran wayarsa ko mayar da sakwannin kar ta kwana da aka aika masa.
SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng