Yanzu Yanzu: Buhari ya tura ministan tsaro taron gaggawa a Chadi
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya tura ministan tsaro, ritaya Birgediya Janar Mansur Dan-Ali zuwa kasar Chadi domin halartan wani taron gaggawa
Dan Ali zai gana da shugaban kasar Chadi, Idris Deby, kan tabarbarewar tsaro a iyakar Najeriya da Chadi.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa a ranar Alhamis, 22 ga watan Nuwamba, Dan Ali ya sanar da shugaban kasar ci gaban da aka samu a fannin tsaro a fadin kasar.
Ya kuma sanar dashi game da kisan wasu sojoji da yan ta’addan Boko Haram suka yi kwanan nan a haanyar iyakar Najeriya da Chadi.
A wani lamari na daban, mun i cewa wani dan kunar bakin wake da ya tarwatsa kansa a wani masallaci da ke cikin sansanin soji a ranar Juma'a, ya yi sanadiyar mutuwar mutane 26 tare da jikkata akalla mutane 50, kamar yadda jami'an tsaro suka fitar da rahoto kan faruwar kai harin.
KU KARANTA KUMA: Kada ku zabi wasu yan siyasa 2 a Najeriya a 2019 – Sani ya gargadi yan Najeriya
Sai dai, har zuwa yanzu, babu wata kungiyar ta'addanci da ta dauki alhakin kai wannan hari.
Wani jami'in tsaro ya bayyana cewa mutanen da lamarin ya afku a kansu, sun taru don gudanar da sallar Juma'a a wani masallaci da ke gundumar Ismail Khel a yankin Khost, Kudancin kasar Afghanistan.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng