Hotuna: Ganduje ya raba taransfoma 100 sakamakon rashin wutan lantarki a sassan jihar Kano
Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullah Umar Ganduje, ya raba na'urar Taransfoma 100 sakamakon rashin wutan lantarki a wurare daban-daban a jihar a yau Juma'a, 23 ga watan Nuwamba, 2018.
Legit.ng ta kawo wannan rahoto ne bisa ga jawabin da babban mai baiwa gwamnan jihar Kano shawara kan labarai, Salihu Tanko Yakassai, ya saki da yammacin yau.
Ya bayyana cewa gwamnan ya sayi wadannan taransfoman ne domin dawo da wutan lantarki wasu wurare a karkara da biranen Kano da suka fuskanci rashin wuta sakamakon rashin Taransfoma.
KU KARANTA: Dan kunar bakin wake ya kashe mutane 26 suna tsakiyar yin salla a cikin masallaci
Yace: "Mai girma gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, a yau ya raba sabbin taransfoma 100 da gwamnatinsa ta siya domin haskaka wurare da dama a Kano da suka shiga duhu sakamakon rashin taransfoma a cikin karkara da biranen jihar."

Source: Facebook

Source: Facebook

Source: Facebook
Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng
Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng