Dan kunar bakin wake ya kashe mutane 26 suna tsakiyar yin salla a cikin masallaci
Wani dan kunar bakin wake da ya tarwatsa kansa a wani masallaci da ke cikin sansanin soji a ranar Juma'a, ya yi sanadiyar mutuwar mutane 26 tare da jikkata akalla mutane 50, kamar yadda jami'an tsaro suka fitar da rahoto kan faruwar kai harin.
Sai dai, har zuwa yanzu, babu wata kungiyar ta'addanci da ta dauki alhakin kai wannan hari.
Wani jami'in tsaro ya bayyana cewa mutanen da lamarin ya afku a kansu, sun taru don gudanar da sallar Juma'a a wani masallaci da ke gundumar Ismail Khel a yankin Khost, Kudancin kasar Afghanistan.
KARANTA WANNAN: Gwamnatin Jigawa ta gina cibiyoyin kiwon lafiya 287 a cikin shekaru 3 - Mataimakin gwamna

Asali: Facebook
Dukkanin wadanda aka kashe a wannan harin kunar bakin waken, suna aiki ma hukumar tsaron kasar Afghanistan ne, a cewar Kaftin Abdullah, mai magana da rundunar soji a Khost, wanda kuma ya bayyana sunansa daya kawai ba tare da na mahaifi ba.
Harin kunar bakin waken na ranar Juma'a ya zo ne kwanaki biyu da wani dan kunar bakin wake ya tarwatsa kansa a wani babban taron maluman addini da aka gudanar a Kabul, babban birnin kasar, wanda ya salwantar da rayuka da dama.
Hukumomi sunce akalla malamai 55 ne aka kashe yayin da 90 suka jikkata a bukin murnar zagayowar ranar haihuwa Manzon Allah (S.A.W), a wani babban dakin taro na kasar.
Mabiya Taliban dai na yakar gwamnatin kasar ne don kakkabe gwamnatin wacce suke ikirarin tana samun gooyon baya daga kasashe turai, da kuma tilasta ficewar jami'an sojin kasashen waje daga cikin kasar ta Afghanistan.
SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng