Tiryan-tiryan: Yadda 'yan Boko Haram suka yi fatata da barikin sojoji na Metele, suka sashe sojoji 75
Daya daga cikin sojojin da suka tsira daga harin da Boko Haram suka kai wa barikin Metele dake karamar hukumar Guzamala a jihar Barno ya bayyana wa majiyarmu ta Premium Times yadda 'yan ta'addan suka yi nasarar yi masu ta'asa a farkon satin nan a barikin su dake a garin Metele.
Sojan wanda ya bukaci a sakaya sunan sa yace shi ma Allah ne ya sa zai tsira da ran sa a wannan hari domin kuwa sojojin Nijeriya da ke aiki a wannan bariki basu ji da dadi ba.

Asali: Twitter
KU KARANTA: Yaki da rashawa: Wani shehin malami yace Buhari ya kama Tinubu
Legit.ng Hausa ta samu cewa kafin wannan hari, sai da Boko Haram suka aika wa sojojin sakon cewa zasu kawo farmaki barikin amma duk da haka da suka zo basu samu wata tujiya ba sakamakon rashin muhimmin shiri kan hakan.
Sojan dai ya fara da labarta cewa: "Boko Haram sun far wa barikin mu ne ranar Litinin da misalin karfe 6 na yamma.
"A lokacin da sojan da ke can kololin sama wato mai hangen nesa daga barikin ya sanar mana cewa ga fa gungun mayakan Boko Haram nan sun kunno kai zuwa wannan bariki sai dukkan mu muka daura damara muka ja daga muna jiran su.
"Gaba daya batakashin bai dauke mu tsawon mintuna 45 ba domin mayakan Boko Haram din sun fi karfin mu a dalilin manyan makamai da suke dauke da su.
"Da muka fahimci cewa ba za mu yi galaba a wannan batakashi da muke yi da ‘yan Boko Hama din ba sai muka nemi mu gudu. Hakan shima yayi mana wuya matuka domin barikin a zagaye yake da yawa sannan kuma ta hanya daya da ake shiga barikin kuma ta nan ne suke bude mana wuta.
"Daya daga cikin matukan motocin yakin mu ya nemi ya bita jikin wannan waya da karfin tsiya. A daidai yana kokarin haka ne motar sa ta kafe a wurin. A nan ne fa Boko Haram suka yi mana kisan kare dangi. Suka rika yi mana barin wuta inda nan take suka kashe kusan duka sojojin dake cikin wadannan motoci da wadanda ke zagaye.
"Wadanda suka samu suka gudu kuwa sun tsinci kan su ne a kauyen Kauwa inda suka yi ta hawa motoci da babura zuwa garin Maiduguri duk kuwa dauke da rauni a jikkunan su.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng