Sarkin Kano Sanusi II ya fayyace gaskiya kan matsayin talauci a Nigeria
- An shirya taron IT don kaddamar da littafi, sai dai taron da ya gudana a Abuja ya dauki wani sabon salo na fede biri har wutsiya kan halin da Nigeria take ciki
- Daga cikin wadanda suka tofa albarkacin bakinsu a taron, akwai Sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi, wanda ya ce Nigeria bata da kudin batarwa don tallafin mai
- Sarkin wanda ya yi nuni da cewa wanda yafi kowa kudi a Afrika dan Nigeria ne, sai dai ya ce kasar ce shelkwatar talauci ta duniya
Sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi, ya ce zai zama abun mamaki, ace kasar Nigeria bata da $3bn zuwa $4bn da zata rinka biya na tallafin man fetur a kowacce shekara, sakamakon yadda talauci yayiwa kasar katutu.
Sanusi Lamido II, ya bayyana hakan a wani taron kaddamar da wani littafi mai suna “From Frying Pan to Fire”, wanda shugaban sashen masu tace labarai a jaridar ThisDay, Mr. Olusegun Adeniyi ya wallafa, taron da ya gudana a birnin tarayya Abuja.
Sarkin wanda ya yi nuni da cewa wanda yafi kowa kudi a Afrika dan Nigeria ne, sai dai ya ce kasar ce shelkwatar talauci ta duniya. A cewarsa, halin da kasar ke tafiya a yanzu, ya sabawa na sauran kasashen da suka ci gaba a duniya.
KARANTA WANNAN: Gwamnatin Kano ta sha alwashin kawo karshen tu'ammali da muggan miyagun kwayoyi

Asali: Depositphotos
Ya ce: "Idan kazo filin sauka da tashi na jirage da ke Abuja, yana cike da jiragen 'yan kasuwa. Idan ka sauka Abuja, sai ka dauka Nigeria wata kasace mai cike da arziki. Muna da tituna masu kyau da gadoji; muna komai a Abuja.
"Amma ka je kauyuka kaga yadda tarin mutanen da ke rayuwa a can. A can ne zaka gane cewa duniyar daban ce. Wannan wani lamarine mai muni da ya kamata mu gyara shi. Dole ne mu kasance masu tuna cewa halin da mutanen kauyen suke ciki, ya shafi kasar baki daya."
Ya kuma yi tsokaci kan yadda ake almubazzaranci da tattalin arzikin kasar da kuma juya baya ga muhimman abubuwa, yana mai jaddada muhimmancin baiwa fannin ilimi fifiko wajen kashe kudaden tallafi, da kuma fannin wuta da masana'antu don samar da ayyukan yi ga jama'a.
A tashi mahangar, Sanusi ya ce 'yan Afrika na bukatar ayyuka kuma suna bukatar rayuwa mai kyau da zata dakatar da su daga ketarewa zuwa wasu kasashen.
SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng