Wani uba ya kashe diyarsa, ya ce Allah ne ya umarce shi

Wani uba ya kashe diyarsa, ya ce Allah ne ya umarce shi

Wani abun tashin hankali ya afku a jihar Benuwe, inda aka samu wani mutum da ya kashe diyarsa mai watanni 9 tare da shaidawa jama'a cewar Allah ne ya umarce shi ya sadaukar da ita.

Wani lamari mai kama da wannan ya taba faruwa a jihar, inda wata mata ta kashe mijinta da yaransu uku.

Depunn, mahaifiyar yarinyar, da yanzu haka ke hannun jami'an 'yan sanda, ya kafe kan cewar bai aikata wani laifi ba saboda Allah ne ya umarce shi ya dauki ran jaririyar.

Mutumin, mai matsakaicin shekaru, ya karbo yarinyar daga hannun mahaifiyarta tare da tafiya da ita wani jeji da ke Mbangur a garin Tse-Agberagba, karamar hukumar Konshisha, inda ya shake ta har lahira.

Wani uba ya kashe diyarsa, ya ce Allah ne ya umarce shi
Wani uba ya kashe diyarsa, ya ce Allah ne ya umarce shi
Asali: Facebook

Bayan ya dawo ba yarinyar ne, sai ya shaidawa jama'a, ba tare da wani ya tambaye shi ba, cewar ya cika umarnin Allah a kan yarinyar.

DUBA WANNAN: Masifar da ta fi Boko Haram na nan tafe a kasar nan - Sarki Sanusi

Wani uba ya kashe diyarsa, ya ce Allah ne ya umarce shi
Wani uba ya kashe diyarsa, ya ce Allah ne ya umarce shi
Asali: Twitter

"Mahaifin yarinyar da kansa ya sanar da jama'a cewar ya kashe diyar sa bisa umarnin ubangiji," a cewar majiyar mu.

Wani shaidar gani da ido ya shaidawa majiyar mu cewar Deppun ya amsa laifin da bakinsa, "tunkiya ta ce kuma na sadaukarwa da ubangiji kamar yadda ya umarce ni. Ban taba dora ko hannu a kan dan wani ba, a saboda haka kar wanda ya ga laifina."

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Benuwe, DSP Moses Yamu, ya tabbatarwa da majiyar mu cewar sun kama mutumin tare da bayyana cewar suna cigaba da bincike a kansa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel