Fadar shugaban kasa ta maka wani malamin addini kotu mai yada karyar mutuwar Buhari

Fadar shugaban kasa ta maka wani malamin addini kotu mai yada karyar mutuwar Buhari

- Malamin addinin da ya ce Buhari ya mutu ya shiga babbar matsala

- Fadar shugaban kasa ta kai karar wani malamin addini kotu dake yada karyar mutuwar Buhari

Mataimaki na musamman ga shugaban kasar Najeriya a kan harkokin shari'a Mista Okoi Obono-Obla ya rubutawa jami'an 'yan sandan farin kaya watau Department of State Services (DSS) da kuma 'yan sandan Najeriya yana kalubalantar wani fasto da laifin yada karairayin mutuwar shugaba Buhammadu Buhari.

Fadar shugaban kasa ta maka wani malamin addini kotu mai yada karyar mutuwar Buhari
Fadar shugaban kasa ta maka wani malamin addini kotu mai yada karyar mutuwar Buhari
Asali: Twitter

KU KARANTA: An damke mutane 3 dake karya da sunan Buhari

Takardun koken da fadar ta shugaban kasa ta rubuta ga jami'an tsaron da kuma majiyar mu ta samu sun nuna cewa an tura su ne a farkon watan nan inda a ciki aka bukaci su binciki wani Bishop Eze Orieka akan zargin yada karairayi akan shugaban kasa.

Legit.ng Hausa ta samu cewa a yan watannin baya dai jama'a da dama musamman ma a kudancin kasar nan sun yi ta yada karairayin cewa wai shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya rasu kuma wai wanda ake gani yanzu ba shi bane wani mai kama da shi ne daga kasar Sudan.

A wani labarin kuma, Da alama dai zaben shekarar 2019 ta raba kawunan Shugabani da kuma dattawan 'yan kabilar Inyamurai musamman ma game da dan takarar da za su marawa baya a zaben dake tafe.

Majiyar mu ta tabbatar mana da cewa yayi da wasu dattawan kabilar daga jihar Imo karkashin jagorancin Sarkin Isuala Mbano suka bayyana cikakken goyon bayan su ga shugaban kasar a zaben, 2019, wasu kuma daga jihar Enugu sun goyi bayan Atiku be.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel