Shugaban NYSC ya roki Ganduje da ya gyara hanyar zuwa sansanin yan batar kasa
Alhaji Ladan Baba, shugaban hukumar bautar kasa (NYSC) a jihar Kano ya roki gwamnatin jihar da ta gyara hanya da ke sada mutum zuwa sansanin yan bauta kasa mai tsawon kilomta biyar a mararrabar Kusalla.
Ya yi kiran ne a ranar Litinin, 19 ga watan Nuwamba lokacin rantsar da yan rukunin Batch ‘C’ stream II a sansanin yan bautarkasa, Kusala a karamar hukumar Karaye da ke jihar.
A cewarsa hanyar bai da kyau don haka yan bautar kasa kan wahala a garuruwan da ke kusa da yankin d ma jami’an NYSC da ke zuwa sansanin.
Don haka ya yi kira ga gwamntin jihar da ta gyara hanyar kamr yadda Gwamna Abdullahi Ganduje ya yi alkawari da farko.

Asali: Depositphotos
Shugaban ya kuma roki gwamnatin jihar da kammala gyaran sansanin baki daya da kuma sanya inji ruwa mai amfani da hasken rana.
KU KARANTA KUMA: Buhari ya gwammaci ace ya fadi maimakon yin magudi a zaben 2019 – Femi Adesina
Ya kuma yaba ma gwamnatin Gaduje bisa namijin kokarin da ta yi wajen gyara hanyar Kano-Gwarzo-Dayi domin a cewarsa shine babban hanyar zuwa Karaye inda anan sansanin yake
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng