Gwamnatin tarayya ta amince da sakin N60bn don gudanar da shirin tallafin shinkafa

Gwamnatin tarayya ta amince da sakin N60bn don gudanar da shirin tallafin shinkafa

- Gwamnatin tarayya ta amince da sakin N60bn don tallafawa shirin tallafin shinkafa, da nufin rage farashin shinkafar a fadin kasar

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya jagoranci taron majalisar zartaswa kan samar da abinci a kasar, da ya gudana a fadar shugaban kasa, ranar Juma'a

- Ministan gona da bunkasa karkara, Mr. Audu Ogbeh ya bayyana cewa ana daf da sake fasalin bankin noma da cewar manoma zasu samu damar sayen hannun jari

Gwamnatin tarayya ta amince da sakin N60bn don tallafawa shirin tallafin shinkafa, da nufin rage farashin shinkafar a fadin kasar. Ministan gona da bunkasa karkara, Mr. Audu Ogbeh ya bayyana hakan a zantawarsa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron majalisar zartaswa kan samar da abinci a kasar.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya jagoranci taron a fadar shugaban kasa, a ranar Juma'a.

Ya bayana cewa ma'aikatar noma za ta kafa wani kwamiti tare da hadin guiwar ma'aikatar kudi don tabbatar da nasarar shirin tallafin shinkafar.

KARANTA WANNAN: Oshiomhole ya gana da Buhari, ya karyata karbar cin hancin $80m don murde zaben APC

Gwamnatin tarayya ta amince da sakin N60bn don gudanar da shirin tallafin shinkafa
Gwamnatin tarayya ta amince da sakin N60bn don gudanar da shirin tallafin shinkafa
Asali: UGC

"Akwai shirin tallafi da ke daf da zuwa. Gwamnati ta amince da sakin N60bn don tallafawa samar da shinkafa da kuma karya farashinta a kasuwannin kasar. Sai dai wannan karon, zamu dauki matakai don gudun bulluwar wata matsala.

"Bama son shiga cikin matsalolin da shirin tallafin man fetur ya samu, don haka akwai kwamitinda zai kula da shirin tare da hadin guiwar ma'aikatar kudi.

"Muna ganin zai zama abu mai muhimmanci mu rantawa manoma, masu raba shinkafar kudade a farashi mai sauki, don tabbatar da cewa uwar kudin bata salwanta ba, idan kuma suka samu riba dai dai gwargwado kuma suka rage farashin kayan, to hakan zai sanya farashin shinkafar a kasuwannin kasar ya fadi warwas.

"Kowacce kasa na yiwa abinci wannan shirin, amma mu zamu yi namu yasha banban da na kowa kuma zaizo cikin sauki ga manoma. Wanda kuma ba zai shafi ribarsu ta yau da kullum ba," a cewarsa.

Ogbeh, wanda ya sanar da cewa ana daf da sake fasalin bankin noma, ya bayyana yakininsa na cewar manoma zasu samu damar sayen hannun jari bayan kammala sake fasalin bankin.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel