Ta bayyana: Yari na shirin amfani da yan kato da gora 8,500 wajen tayar da tarzoma a zaben 2019

Ta bayyana: Yari na shirin amfani da yan kato da gora 8,500 wajen tayar da tarzoma a zaben 2019

Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan man fetur, Sanata Kabiru Marafa, ya bayyana cewa gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari na shirin amfani da matasa da sunan yan kato da gora wajen daburta zaben 2019 a jihar Zamfara.

Bayan rikicin da yaki ci yaki cinyewa kan zaben fidda gwanin jihar karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), gwamna Yari ya alanta daukan sabbin yan kato da gora 8,500, da sunan amfani da su wajen kawo karshen garkuwa da mutane da kashe-kashe jihar.

Marafa, wanda shi ma dan takaran gwamna ne a jihar Zamfara, ya nuna mamakinsa kan yadda gwamna Yari wanda ya bari yan baranda suka hallaka al’ummar jihar kuma ya haramta ayyukan yan banga da yan kato da gora duk da kukan jama’ar jihar, zai sanar da daukan matasa 8,500 a karshen wa’adinsa.

KU KARANTA: Rikici ya kaure har ta kai a cinnawa fadar Sarkin Abi wuta

Yace: “Daga bincikenmu daga na kusa da shi, Yari ya dauki matasa 8,500 domin shirya tada tarzoma a zaben 2019 a jihar Zamfar, kamar yadda ya yi a zaben fidda gwanin jihar da akayi a ranan 3 ga watan Oktoba inda aka rasa rayuka shida kuma da yawa suka jikkata.”

“Saboda gazawarsa a jihar, Yari yayi tunanin zai yi amfani da karfin sama wanda ya hada da jami’an tsaro a zaben bana, amma hakan ba zai yiwu ba tunda hukumar INEC tace ba zata amshi kowani sunan dan takarar APC daga jihar ba.”

Ya yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari da hukumomin tsaro da su sanya baki wajen hana Yari baiwa matasa makamai domin cimma burinsa na siyasa.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel