Allah kare bala'i: Annobar amai da zawo tayi mummunar barna a Arewa maso gabas

Allah kare bala'i: Annobar amai da zawo tayi mummunar barna a Arewa maso gabas

Hukumar dake tallafawa 'yan gudun hijira ta gwamnatin kasat Norway watau Norwegian Refugee Council, (NRC) a turance ta bayyana cewa annobar cutar amai da zawo ta kashe akalla mutane 175 a jahohin Borno, Adamawa da Yobe tare da kwantar da kusan mutane dubu 10 a asibiti.

Haka zalika hukumar ta alakanta bulla tare da yaduwar cutar da yawa tare da cunkoson da ke a akwai a sansanonin 'yan gudun hijirar da aka ware wa wadanda ibtila'in rikicin ta'addancin Boko Haram ya rutsa da su.

Allah kare bala'i: Annobar amai da zawo tayi mummunar barna a Arewa maso gabas
Allah kare bala'i: Annobar amai da zawo tayi mummunar barna a Arewa maso gabas
Asali: UGC

KU KARANTA: Hotunan idan aka gwabza yakin duniya na 1

Legit.ng ta samu cewa wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da shugaban ayyukan jin kai na hukumar dake a yankin Arewa maso gabashin kasar nan Janet Chenero ta fitar tana mai rokon agajin gaugawa domin rage radadin hakan.

A wani labarin kuma, daya daga cikin wadanda suka nemi takarar kujerar Gwamnan jihar Kaduna a karkashin jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Muhammad Sani Bello ya sanar da ficewar sa daga jam'iyyar, kamar dai yadda muka samu daga majiyar mu.

Muhammad Sani, ya bayyana wannan matsayar da ya dauka ne a garin Kaduna ranar Litinin din da ta gabata a gidan sa yayin da ya kira wani dan kwarya-kwaryan taron manema labarai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng