Iko sai Allah: Ku sadu da wata kyakkyawar mata da ke soyayya da fatalwa

Iko sai Allah: Ku sadu da wata kyakkyawar mata da ke soyayya da fatalwa

Wata ta bar dubun dubatar al'umma a cikin al'ajabi bayan da ta ce ita da saurayin ta fatalwa ne kuma tuni har sun kammala shire-shiren yin aure a tsakanin su cikin kankanin lokaci.

Matar, baturiya 'yar kasar Birtaniya mai suna Amethyst Realm kuma kuma mai shekaru 30 a duniya ta bayyana hakan ne a cikin wani shirin gidan Talabijin da aka kira ta a matsayin bakuwa.

Iko sai Allah: Ku sadu da wata kyakkyawar mata da ke soyayya da fatalwa

Iko sai Allah: Ku sadu da wata kyakkyawar mata da ke soyayya da fatalwa
Source: UGC

KU KARANTA: Rahama Sadau ta hadu da masoyin ta a dandalin sada zumunta

Legit.ng Hausa ta kasa samun cewa wani abun al'ajabin kuma da ya kara jefa jama'a cikin mamaki shine da tace ita daman can ta saba yin soyayya da fatalwowi domin kuwa akalla ta kwanta da fatalwowin akalla 20 tun bayan balagar ta.

Amethyst Realm ta kara da bayyanawa a cikin firar da akayi da ita cewa wannan saurayin nata na yanzu sun hadu ne a kasar Australia a shekarun baya kuma yanzu sun fahimci juna sosai.

Daman dai Hausawa sunce, inda ranka, to kana da sauran kallo.

Ko me za ku ce game da hakan?

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel