Babbar magana: INEC ta cika alkawarinta na haramtawa APC gabatar da 'yan takara a jihar Zamfara

Babbar magana: INEC ta cika alkawarinta na haramtawa APC gabatar da 'yan takara a jihar Zamfara

- Hukumar INEC, a jihar Zamfara, ta wallafa sunayen 'yan takarar kujerar gwamna, da na 'yan majalisun dokoki na jihar ba tare da sanya 'yan takara daga jam'iyyar APC ba

- Jam'iyyun da hukumar INEC ta wallafa sunayen 'yan takararsu a jihar sun hada da; APGA, PDP, NRM, SDP, PRP, GPN and NCP da dai sauransu

- "Har yanzu lamarin yana kotu, kuma idan har kotu ta bamu umurni na mu sanya yan takarar APC a ciki lissafi, dole ne mu bi umurnin kotu," a cewar kwamishiniyar hukumar

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, a jihar Zamfara, ta wallafa sunayen 'yan takarar kujerar gwamna, da na 'yan majalisun dokoki na jihar da su yi takara a babban zaben 2019. Sai dai hukumar ta wallafa sunayen ne ba tare da sanya 'yan takara ko daya daga jam'iyyar APC ba.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, ya bayar da rahoton cewa an nemi sunayen 'yan takara daga jam'iyyar APC an rasa a sunayen da hukumar ta wallafa a allon sanarwa da ke cikim sakatariyarta da ke Gusau, a ranar Juma'a.

Jam'iyyun da hukumar INEC ta wallafa sunayen 'yan takararsu a jihar sun hada da; APGA, PDP, NRM, SDP, PRP, GPN and NCP da dai sauransu.

KARANTA WANNAN: An gurfanar da jami'in rundunar 'yan sanda da ake zargin ya kashe Miss Anita Akapson

Babbar magana: INEC ta cika alkawarinta na haramtawa APC gabatar da 'yan takara a jihar Zamfara
Babbar magana: INEC ta cika alkawarinta na haramtawa APC gabatar da 'yan takara a jihar Zamfara
Asali: Depositphotos

Da ta ke jawabi ga manema labarai a Gusau, kwamishiniyar hukumar ta kasa mai kula da jihohin Sokoto, Kebbi da Zamfara, Hajiya Amina Zakari wacce ta kai ziyarar aiki a jihar, ta ce hukumar bata karbi sunayen 'yan takara daga jam'iyyar APC ba.

"Ina tunanin, sau tari an sha fada cewa APC bata da yan takara a jihar, don haka mu bamu karbi sunayen yan takara na jam'iyyar ba."

"Duk da cewa har yanzu lamarin yana kotu, kuma idan har kotu ta bamu umurni na mu sanya yan takarar APC a ciki lissafi, dole ne mu bi umurnin kotu," a cewar ta..

Zakari ta ce ta kai ziyara jihar Zamfara ne don ganewa idanuwanta yadda ofishin hukumar INEC ke gudanar da ayyukansa, tare da kuma sanya ido kan yadda hukumar ke ci gba da fitar da sunayen wadanda suka yi rejistar zabe, dama karbar katin zaben nasu.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel