Hukumar Kwastam ta damke kwantena cike kayan Sojoji da makamai a jihar Ribas

Hukumar Kwastam ta damke kwantena cike kayan Sojoji da makamai a jihar Ribas

Hukumar Kwastam na Najeriya, shiyar tashan jirgin ruwan Onne sun damke kwantena dauke da rigunan sojoji 600, hulunan sojoji 600 da takalman sojoji 600.

An shirya kayayyakin sojin ne nade jikin tiyo 80, katon na yar ciki 10, katon na takalma 50, katon da tile 207, dilan safa 15, da addun 575.

Hukumar ta bayyana cewa an damke wasu mutane dake da alaka da wadannan kaya da aka kama kuma an turasu hedkwatan kwastam dake Abuja domin bincike.

Kakakin hukumar, Ifeoma Onuigbo, ta bayyana hakan ne a wani jawabi da ta saki jiya inda tace shugaban ynkin, Kontrola Aliyu Galadima Saidu, ya nuna bacin ransa kan yawaitan irin wadannan abubuwa.

KU KARANTA: Shekau ya mayar da martani ga wadanda suka ce ya mutu (Bidiyo)

Daga cikin abubuwan da aka damke sune jarkan man gyad 1,070, buhun shinkafa 50, rabin buhun shinkafa 1,040, buhun shinkafa kilo goma guda 19,680.

Bugu da kari, an damke katon na tumatirin gwangwani 3,560, buhun shinkafan gwamnati 196, dilan gwanjo 30, dilan takalma 3 da sauransu.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel